Sunaye: Gimbiya da dan shekara 1 daga cikin iyalin sarkin Kajuru dake hannun 'yan bindiga
- Bayan sa'o'i ashirin da hudu da sace Sarkin Kajuru, 'yan bindiga sun sako shi
- Sai dai sarkin kadai suka sako yayin da suka rike sauran mutane 13 da suka sata
- Daga cikin mutum goma sha ukun akwai gimbiya 1 tare da yaro mai shekara 1 a duniya
Bayan sa'o'i ashirin da hudu da sace Sarki Alhaji Alhassan Adamu na Kajuru, 'yan bindiga sun sako shi tare da mika shi ga iyalinsa.
A ranar Lahadi, wasu miyagun 'yan bindiga sun shiga har cikin gidan sarautar Kajuru inda suka sace sarki tare da wasu mutum 13.
Sai dai 'yan biindigan sun sako sarkin tare da rike gimbiya daya da sauran wadanda suka sace, Daily Trust ta ruwaito.
KU KARANTA: Hotuna da bidiyon Ahmed Musa tare da dalleliyar sabuwar amaryarsa sun bayyana
KU KARANTA: Dalla-dalla: Gagarumin Luguden Wuta na Sa'a 1 aka yi Kafin Sace Sarkin Kajuru
Daga cikin wadanda 'yan bindigan suka rike akwai gimbiya, diyar sarkin guda daya mai suna Zainab da kuma yaro karami mai shekara daya kacal a duniya.
Ga jerin sunayen wadanda har yanzu ke hannun 'yan bindigan:
Zainab Alhassan (diyar sarki)
Zainab Mukhtar, (jika)
Muhammad Sa’adanu (jika)
Salim Musa (jika)
Faisal Musa (jika)
Ahmed Mukhtar (jika)
Suleiman Umar (Mai sarauta)
Nazifi Rayyanu
Ayuba Yunusa
Amina Abubakar
Maryam Abubakar
Mardiyya Sani
Mudassir Sani (yaro mai shekara 1)
'Yan bindiga sun bada hakuri
Kamar yadda daya daga cikin wadanda suka karbo sarkin ya bayyana, ya ce miyagun 'yan bindigan sun kira su kan su zo su karba sarkin da yammaci,
Bayan isarsu, sun samu 'yan bindiga dauke da makamai kuma sanye da kayan sojoji inda suka dinga bada hakuri kan abinda suka yi.
'Yan bindigan sun tabbatar da cewa basu samu natsuwa da kwanciyar hankali ba tun bayan da suka saci basaraken a ranar Lahadi, Daily Trust ta wallafa.
A wani labari na daban, Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya musanta rahoton dake yawo na nada gwamna a wasu yankunan jihar Borno da Boko Haram tare da ISWAP suka yi.
A makon da ya gabata, bidiyon da ake zargin na nada gwamnan Boko Haram a Borno ne ya dinga yawo a kafafen sada zumuntar zamani, Daily Trust ta ruwaito.
Hukumar rikon kwarya ta 'yan ta'addan ta samu shugabancin wani Abba Kaka, wanda aka nada a matsayin shugaban wasu yankunan Borno.
Asali: Legit.ng