Calabria: Hotunan gari a Italy da zasu bada N13.6m ga masu son komawa da zama
- Wani kauye a kasar Italia ya shirya baiwa duk mai son komawa da zama kudi har N13.6 miliyan
- Wannan kudin da yankin Calabria zai bada yana yin hakan ne domin habaka yawan masu zama ciki
- Baya ga wannan makuden kudin da za a baiwa mai son zama, akwai yuwuwar a bada jari domin fara kasuwanci
Yankin Calabria na kasar Italiya ya shirya baiwa duk wanda zai tattara komatsansa ya koma garin da zama kudi har N13.6 miliyan, CNN ta ruwaito.
Za a bada wannan kudin ne na tsawon shekaru uku kuma ana son hakan ta janyo hankalin jama'a wurin komawa garin gaba daya.
KU KARANTA: Rikici ya barke tsakanin iyalin Yar'adua da Mijin tsohuwar matar Danbaba Suntai
KU KARANTA: Bayan Kammala Mukabala, za a Gurfanar da Abduljabbar Kabara Gaban Kotu
Ana wannan kokarin ne domin shawo kan matsalar rashin mutane da kauyen ke fuskanta na tsawon shekaru kuma a habaka yawan kauyen mai mazauna 2,000.
Garin yana maraba da mutane masu shekaru ba sama da arba'in ba da haihuwa a duniya.
Sharudan da za a cike kafin a samu N13.6 miliyan
Baya ga cike sharadin dole na komawa garin cikin kwanaki casa'in da nema, dole ne wanda zai zauna ya shirya kafa kasuwanci ko kuma cigaba da wani kasuwanci na garin.
Wani shugaba a yankin mai suna Gianluca Gallo yayin tattaunawa da CNN ya ce akwai yuwuwar a kaddamar da wani tallafi domin kafa cibiyar kasuwanci.
Ya ce: "Muna ta shirye-shirye, watannin tare da lokacin da za a dauka ko kuma za a hada da kauyuka masu mazauna 3,000. A halin yanzu kauyuka masu yawa sun nuna bukatar jama'a kuma muna fatan idan wannan ya fara aiki, sauran zasu biyo baya."
Luxury Launches ta bayyana biranen da suka shiga tsarin neman jama'a da: Aieta, Albidonia, Bova, Caccuri, Civita, Samo and Precacore, Sant’Agata del Bianco, San Donato di Ninea da Santa Severina.
A wani labari na daban, kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar APC na kasa, ya rushe kwamitin shugabannin jam'iyyar na jihar Zamfara.
Sanata John Akpanuodedehe, sakataren CECPC na kasa, ya sanar da rushewar a wata wasika mai kwanan wata 9 ga Yulin 2021 kuma aka aikata ga shugaban kwamitin rikon kwaryan da aka rushe, Lawal Liman.
Kwafin wasikar wacce aka baiwa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a ranar Lahadi a garin Gusau, ta ce an rushe kwamitin a take ne.
Asali: Legit.ng