COVID-19: Yadda Najeriya ta kunyata masana - Aregbesola
- Ministan cikin gida ya nuna yadda Najeriya ta kunyata hasashen masana kan illar da COVID-19 za ta yi wa kasar
- Ya ce matakan da gwamnatin tarayya ta dauka sun taimaka wajen dakile tasirin annobar
- Aregbesola ya nunar da cewa gwamnatin ta kuma yi kokarin tallafa wa gajiyayyu bayan annobar
Ministan harkokin cikin Gida, Rauf Aregbesola, ya ce tabbas Gwamnatin Tarayya ta kunyata masana wadanda suka yi hasashen cewa Najeriya da sauran kasashen Afirka za su durkushe a sakamakon mummunan tasiri kan tattalin arzikin da cutar COVID-19 za ta haifar.
Daraktan yada labarai na ma’aikatar cikin gida, Misis Blessing Lere-Adams, ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Litinin a Abuja.
A cewarta, Ministan ya yi wannan ikirarin ne a lokacin da yake gabatar da lakcar shekara-shekara karo na uku na Jami’ar Ekiti, da ke Ado Ekiti, mai taken, “COVID-19: Tattalin Arziki da Tsaro”, rahoton Punch.
'Yan bindiga sun gano rashin tasirin hada lamabobin SIM da NIN, ‘yan sanda ba sa iya bin sawun 'yan bindiga
Aregbesola ya bayyana cewa aiwatar da manufofin da ba na magunguna ba da suka hada da kulle da killacewa da dakatar da zirga-zirga tsakanin jihohin kasar nan da kiyaye bada tazarar jama'a da sanya kyallen fuska da wayar da kan jama'a, sun tabbatar da yin tasiri sosai wajen dakatar da yaduwar cutar.
“Annobar ta addabe mu amma gwamnati ta iya takaita illarta,” inji Ministan.
DUBA NAN: Yadda zamu ceto ‘yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci – Osinbajo
KU DUBA: Magoya bayan Buhari ba za su taba barin Tinubu ya zama Shugaban Kasa ba – Lamido
Ministan ya ce asarar rayukan da aka samu, duk da cewa abin a yi nadama a kanshi ne, dangane da hasashen Gidauniyar Bill and Melinda Gates da kuma Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) cewa Najeriya, da sauran kasashe masu tasowa, za ta yi fama da mummunan tasiri sakamakon cutar.
Ya ce daga baya an bayar da rahoton cewa Bill Gates ya cika da farin ciki cewa hasashen da aka yi ya zama shifcin gizo.
Ya kuma yabawa masana kimiyya da sauran jami’ai a bangaren kiwon lafiya kan yadda suka magance cutar tare da samar da allurar riga-kafi a cikin lokaci dan taimakawa bil Adama.
Daga nan Aregbesola ya bukaci ‘yan Najeriya da su fito kwansu da kwarkwatarsu domin yin allurar rigakafi a cibiyoyin rigakafin da ke fadin kasar.
Su Dangote da Isyaka Rabiu sun yi kokari
Dangane da tattalin arziki, Ministan ya yaba da kokarin da masu zaman kansu ke jagoranta game da COVID-19 (CACOVID) saboda gagarumin aikin da aka yi don taimakawa gwamnati da 'yan Najeriya wajen yaki da cutar.
Ya kuma tuna cewa a watan Afrilu na shekarar 2020, Gwamnatin Tarayya ta fara tura N20,000 ga magidanta talakawa da marasa karfi da aka yi wa rajista a karkashin shirin National Social Register (NSR).
Tun da farko, Mataimakin Shugaban Jami’ar, Farfesa Edward Olanikeku, ya yaba wa Ministan bisa girmama gayyatar da makarantar ta yi masa.
Asali: Legit.ng