Masarautar Katsina: Abin da ya sa mu ka dakatar da bikin hawan Sallah a bana

Masarautar Katsina: Abin da ya sa mu ka dakatar da bikin hawan Sallah a bana

- Sarkin Katsina ya kashe bukukuwan hawan sallah a wannan shekara

- Abdulmumin Kabiru Usman ya bayyana wannan a wata sanarwa jiya

- Mai martaba ya ce za ayi amfani da lokacin wajen yi wa kasa addu’o'i

Mai martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumin Kabiru Usman CFR, ya bada sanarwar ba za a gudanar da bukukuwan hawan sallah a shekarar bana ba.

Abdulmumin Kabiru Usman ya sanar da daukacin mutanen Katsina cewa matsalar sace-sace da kashe-kashen da ake yi ya sa aka dauki wannan matakin.

Sarkin ya bayyana cewa shawarwarin da ya samu daga gwamnati, jami’an tsaro da ma’aikatan lafiya suka sa aka yi watsi da shagulgulan karamar sallah.

KU KARANTA: Masarautar Kano za ta yi hawan durbar a bana - Sarki

Katsina da wasu daga cikin makwabtanta suna fuskantar matsalar ta’adin ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane da suka adddabi yankunan jihohin Arewan.

Da zarar an sauko daga idi, kowane Hakimi zai wuce gidansa. “Masarautar ta yanke shawarar ba za ta gudanar da hawan sallah da duk wasu shagulgula ba.”

Bayan matsalar rashin tsaro da ake fama da shi, gwamnatin Najeriya ta na kaffa-kaffa a kan samun cunkoson jama’a lokacin bikin saboda annobar COVID-19.

Sanarwar masarautar take cewa: “Amma za a gudanar da sallar idi kamar yadda aka saba.”

KU KARANTA: Buhari zai yi bikin sallarsa ne a fadar Aso Rock

Masarautar Katsina: Abin da ya sa mu ka dakatar da bikin hawan Sallah a bana
Sarkin Katsina Hoto: Abdulmumini Kabir Usman
Asali: Twitter

“Sannan za a gudanar da addu’o’in neman zaman lafiya. Mu na rokon Allah (SWT) madaukakin Sarki ya zaunar da Katsina da ma kasar mu gaba daya lafiya.”

Sanarwar ta fito ne daga bakin Sakataren masarautar kasar Katsina, Alhaji Bello Mamman Ifo, wanda shi ne ya ke rike da sarautar Sarkin Yakin Katsina.

Bello Mamman Ifo ya aika wannan takarda ne ga manema labarai a ranar Litinin, 10 ga watan Mayu, 2021, domin a sanar da daukacin al’ummar Katsina.

A shekarar nan, kun ji cewa Zazzagawa za su yi Sallar Idi a filin Mallawa. Wannan ne zai zama karon farko cikin shekara 62 da Sarki ya yi idi a wannan fili.

Tarihi ya nuna cewa tun kafin Sarki Muhammadu Aminu wanda ya yi shekaru 16, da Shehu Idris da ya shafe shekaru 46 rabon da ayi sallah a wajen Kofar Doka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel