An kuma: Bidiyon Zukekiyar Baturiya da ta Dira a Najeriya Domin Masoyinta ya bazu
- Wasu masoya biyu sun nunawa duniya cewa soyayya ta wuce karfin launin fata ko kasa kuma so makaho ne
- Baturiyar matar ta bar kasarta inda ta dira Najeriya saboda ta samu ganin masoyinta dan Najeriya
- A wani bidiyon masoyan, an gansu suna shagali tare da soyewa tare, lamarin da ya janyo maganganu a kafar sada zumunta
Wasu masoya biyu sun jijjiga kafafen sada zumunta da salon soyayyarsu. Abinda ya fi baiwa jama'a mamaki kuma yasa suka dinga magana shine ganin banbancin launin fatarsu.
@gossipboyz1 ta wallafa bidiyon a Instagram kuma tana bada labarin yadda baturiyar ta garzayo har Najeriya domin haduwa da masoyinta.
KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da Sarkin Kajuru tare da iyalansa 13
KU KARANTA: Bayan Kammala Mukabala, za a Gurfanar da Abduljabbar Kabara Gaban Kotu
Shafin ya wallafa: "Soyayya ruwan zuma, bata san nisa ba. Ta garzayo daga Turai har Najeriya domin haduwa da masoyinta."
'Yan Najeriya sun yi martani
@_blingsexchange martani tayi da: "Abu kadan da muke jira mu yi wuff... Ba haka ake yi ba fa."
@yemishark rubutawa tayi: "Soyayya tana da dadi irin haka. Baba zai tsere..."
@king_vicky_tyann tsokaci yayi da: "A ina kuke nemo irin wannan soyayyar, ina zan samu so na gaskiya.?"
@xtian_crystal mamaki tayi tare da cewa: "A ina kuke ganin irin wannan soyayyar?"
A wani labari na daban, kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar APC na kasa, ya rushe kwamitin shugabannin jam'iyyar na jihar Zamfara.
Sanata John Akpanuodedehe, sakataren CECPC na kasa, ya sanar da rushewar a wata wasika mai kwanan wata 9 ga Yulin 2021 kuma aka aikata ga shugaban kwamitin rikon kwaryan da aka rushe, Lawal Liman.
Kwafin wasikar wacce aka baiwa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a ranar Lahadi a garin Gusau, ta ce an rushe kwamitin a take ne.
"Na rubuto in sanar da ku cigaban da aka samu a cikin jam'iyyarmu a jihar. Kwamitin rikon kwarya na kasa ya amince da rushe dukkan shugabanni jam'iyyar a matakin gunduma, karamar hukuma da jiha baki daya.
“Wannan cigaban zai fara aiki ne a take," wasikar tace.
Asali: Legit.ng