Hakan jahilci ne: Minista Malami ya caccaki lauyan turai da ya kare Nnamdi Kanu

Hakan jahilci ne: Minista Malami ya caccaki lauyan turai da ya kare Nnamdi Kanu

  • Ministan shari'a, Abubakar Malami ya caccaki lauyan kasar wajen da ya goyi bayan Nnamdi Kanu
  • Ya kira shi da jahili ya kuma ce lallai ya koma makaranta kafin lokaci ya kure masa a nan gaba
  • Hakazalika ya ce, ya gagara zama shahararre a Najeriya wannan yasa ya gudu ya koma kasar waje

Kelechi Amadi ya hadu da fushin Ministan Sharia game da kalamansa kan kama Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar IPOB.

Ministan na kasar Kanada ya sha caccaka daga babban lauyan tarayya kuma ministan shari’a, Abubakar Malami inda ya yi masa wankin babban bargo, inji rahoton The Cable.

A kwanakin baya ne Madu ya caccaki Minista Malami game da kamun Nnamdi, yana mai cewa idan har da gaske an kama Kanu ba bisa ka'ida ba aka dawo da shi Najeriya, to Malami ya zama abun kunya ga doka da oda.

KARANTA WANNAN: Shugaba Buhari ya jinjina wa jami'an tsaro bisa kame Nnamdi Kanu da farautar Igboho

Baka san me kake ba: Minista Malami ya caccaki lauyan turai da ya kare Nnamdi Kanu
Ministan shari'a, Abubakar Malami | Hoto: bbc.com
Asali: UGC

A nasa martanin, Minista Malami ya bayyana Madu a matsayin wanda bai san me yake ba kuma jahili, Daily Trust ta kara da cewa.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Dakta Umar Gwandu, mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai ga ministan.

Ya ce:

“Babban Lauyan na Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami (SAN) ya bayyana ra'ayoyin da aka danganta ga wani Kelechi Madu a matsayin ra’ayoyin jahilci wanda suka wuce kima kuma sun saba da aikin doka

Malami ya ce

"Abin takaici ne a matsayinsa na Babban Lauya Janar na wani lardi, Madu ya kasa fahimtar sanin manyan dokokin kasarsa inda yake zaune da kuma dokokin kasa da kasa."
"Kamar yadda maganar take 'dokin mai magana ya fi gudu'. Muna ba da shawara ga (Lauyan) wanda ake kira 'mai ilmi' da ya sauke girman kai kuma ya koma karatun littattafan shari'a kafin ya bude bakinsa don ya tozarta kansa a idon al'umma masu tunani mai kyau wanda hakan ke jawo wa kansa zargin da zai iya haifar da shakku game da cancantarsa a aikin da yake ikirarin yana yi a yanzu, bayan ficewa daga kasarsa ta asali inda ya kasa yin fice. ".

Ghali Na'Abba Ya Yi Martani Kan Kame Nnamdi Kanu da Farautar Sunday Igboho

Ghali Na’Abba, tsohon kakakin majalisar wakilai, ya ce yana goyon bayan matakin da gwamnatin tarayya ta dauka a kan Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar IPOB da kuma Sunday Igboho, dan gwagwarmayar kafa kasar Yarbawa, The Cable ta ruwaito.

Na’abba, wanda shine shugaban kungiyar tuntuba ta Najeriya (NCFront), ya fadi hakan ne a matsayin martani ga wata sanarwa daga Olawale Okunniyi, sakataren kungiyar.

Okunniyi ya ce NCFront za ta kare Yarbawa masu zanga-zanga a kotu, biyo bayan kame wasu adadi na masu zanga-zangar a karshen mako a jihar Legas.

KARANTA WANNAN: Da duminsa: Bayan da kotu ta wanke ta kan batun NYSC, ministar Buhari ta yi martani

Lamari ya yi zafi: Sarkin Yarbawa ya shawarci Sunday Igboho ya mika kansa ga DSS

A wani labarin, Jihar Osun - Sarkin gargajiya, Olowu Kuta kuma Shugaban Majalisar koli ta Owu Obas, Oba Hameed Makama, ya shawarci mai rajin kare hakkin Yarbawa, Sunday Ighoho, da ya mika kansa ga Ma’aikatar Tsaro ta Farin Kaya (DSS).

Sarkin ya bayyana haka ne a fadarsa dake Owu Kuta a karamar hukumar Aiyedire a jihar Osun yayin hira da manema labarai.

Ya shawarci masu fafutukar ballewar da su tattaunawa da Gwamnatin Tarayya, The Nation ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel