Kasar Larabawa ta kirkiri manhajar soyayya don hada aure daidai da tsarin Muslunci

Kasar Larabawa ta kirkiri manhajar soyayya don hada aure daidai da tsarin Muslunci

  • Kasar Iran ta kirkira wata manhajar hada ma'aurata wacce za ta hada masu son yin aure da gaske
  • Kasar ta gindaya wasu hsarudda wajen amfani da wannar manhaja, wacce sai an yi gwaji kafin ayi amfani da ita
  • Irin wadannan manhajoji sun samu karbuwa a kasar Iran, musamman ma waje hada aure a kasar

Mahukunta a kasar Iran sun kaddamar da wata manhaja ta soyayya wadda suka ce nufinta shi ne ta saukake neman aure bisa tsarin addinin Musulunci, BBC Hausa ta ruwaito.

Hukumar yada manufofin addinin Musulunci ta kasar ce ta kirkiro manhajar mai suna Hamdam wadda ke nufin aboki ko abokiyar zama, AlJazeera ta ruwaito makamancin haka.

Manhajar tana amfani da basirar komfuta wajen hada wadanda suke son su yi aure, kodayake mata daya kacal aka amince wa namiji ya aura.

KARANTA WANNAN: Hotuna: Shugaba Buhari ya karbi gwamnonin PDP da suka sauya sheka zuwa APC

Kara karanta wannan

Hotuna: Shugaba Buhari ya karbi gwamnonin PDP da suka sauya sheka zuwa APC

Kasar Larabawa ta kirkiri manhajar soyayya don hada aure a daidai da tsarin Muslunci
Balarabiya rike da wayar salula | Hoto: bbc.com/hausa
Asali: UGC

Haka kuma, sai an yi wa wadanda suke son su yi amfani da manhajar gwaji domin a tabbatar da cewa ba su da damuwa a kwakwalwarsu kafin a ba su damar amfani da ita.

Manhajojin soyayya sun samu karbuwa sosai a Iran amma yanzu wannan ce kadai ce halattacciyya.

Wani dan Najeriya ya kirkiri hanyar samawa matasa aiki a Amurka

Wani Ba’amurke dan asalin kasar Najeriya, Dakta Henry Balogun, ya jagoranci wani dandalin yanar gizo don rage rashin aikin yi a Najeriya, ta hanyar neman guraben aiki a duniya, ga daliban da suka kammala karatun su na Najeriya.

Balogun, haifaffen Ikere dake Jihar Ekiti ne kuma ya zauna a Amurka sama da shekaru 40, ya ce yana bayar da ayyukan ne ba tare da karbar anini ba, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

A cewarsa, kokarin na zuwa ne ta dandalinsa na yanar gizo, www.primehangout.com, wanda ke taimakawa wadanda suka kammala karatu, musamman wadanda suka fito daga Najeriya wadanda ke bukatar aiki, don samun abun yi.

Kara karanta wannan

Daga ƙarshe, an kama wanda ya kitsa kisar gillar da aka yi wa Shugaba Moise

KARANTA WANNAN: Aikin Kwangila: Barazanar da Ma’aikatan Banki Ke Fuskanta Na Karancin Albashi

Yadda 'yan gudun hijira suka haifi jarirai sama da 17000 a sansani a jihar Borno

A wani labarin, Kungiyar kula da 'yan gudun hijira ta duniya ta ce an haifi jarirai 17,053 a sansanonin 'yan gudun hijira na Jihar Borno kakai cikin shekaru uku, BBC Hausa ta ruwaito.

Kungiyar ta Majalisar Dinkin Duniya (MDD) mai suna International Organisation for Migration (IOM), ta fada wa kamfanin labarai na NAN cewa an haifi yaran ne a sansani 18 da ke jihar, wadanda kuma aka yi wa rajista daga 2019 zuwa watan Mayun 2021.

Mista Frantz Celestin wanda shi ne shugaban IOM, ya ce sun hada gwiwa da hukumar kidaya ta Najeriya da kuma asusun yara na MDD domin sama wa jariran takardun haihuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel