Da Ɗuminsa: Gwamnonin Kudu Maso Yamma Ne Suka Ɓoye Sunday Igboho, Miyetti Allah

Da Ɗuminsa: Gwamnonin Kudu Maso Yamma Ne Suka Ɓoye Sunday Igboho, Miyetti Allah

  • Miyetti Allah ta yi ikirarin cewa gwamnoni shida na yankin kudu maso yamma ke bawa Sunday Igboho kariya
  • Mai magana da yawun kungiyar, Saleh Alhassan, ne ya sanar da hakan a ranar Litinin ya kuma bukaci gwamnonin su fito da dan gwagwarmayar da ake nema ruwa a jallo
  • Idan za a iya tunawa, a ranar Alhamis 1 ga watan Yuli ne hukumar yan sandan farin kaya DSS ta ayyana nemansa ruwa a jallo bayan samame da ta kai a gidansa da ke Ibadan

An zargi gwamnoni kudu maso yamma da boye dan gwagwarmaya Sunday Igboho a yayin da hukumar yan sandan farin kaya ta DSS ke namansa ruwa a jallo.

Miyetti Allah Kautal H*re, daya daga cikin kungiyoyin makiyaya a Nigeria ne ta yi wannan zargin yayin wani tattaunawa da ta yi da The Punch a ranar Litinin 12 ga watan Yuli.

Da Duminsa: Gwamnonin Kudu Maso Yamma Ne Suka Boye Sunday Igboho, Miyetti Allah
Da Duminsa: Gwamnonin Kudu Maso Yamma Ne Suka Boye Sunday Igboho, Miyetti Allah. Photo credit: Sunday Igboho fans
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Da Ɗuminsa: Ƴan Bindiga Sun Turo Mana Bidiyon Yadda Suka Aurar Da Ƴaƴanmu Mata, Iyayen Ɗaliban Kebbi

Kara karanta wannan

Shugabancin Kasa: Yeriman Bakura ya magantu kan tsayawa takara a 2023 karkashin APC

Saleh Alhassan, mai magana da yawun kungiyar ya yi zargin cewa gwamnoni shida na jihohin kudu maso yamma ne suke boye Igboho.

A cewar Alhassan, ana amfani da Igboho ne da kuma gwagwarmayar siyasan da ya ke yi. Ya kara da cewa duk da gwamnonin sun boye shi, jami'an tsaro za su kamo shi.

Ya kara da cewa iyayen gidan Igboho wato gwamnonin kudu maso yamma su fito da shi.

Amma, Donald Ojogo, hadimin gwamna Rotimi Akeredolu kuma shugaban kungiyar gwamnonin jihohin kudu maso yamma, a martaninsa, ya ce ba mutuncin gwamnonin bane ma su yi martani kan wannan zargin.

KU KARANTA: Kotu za ta bada umurni a kamo mata tsohuwar Ministan Nigeria da ake zargi da handame dukiyar al'umma

Ba a san inda dan gwagwarmayar na Yarbawa ya shiga ba tun bayan samamen da jami'an DSS suka kai gidansa a farkon wannan watan.

'Yan Sanda da Jami’an DSS Sun Yi Wa Cocin Dunamis Ƙawanya a Abuja

Kara karanta wannan

Ba a fahimce ni bane: Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya nemi afuwa

A wani labarin daban, kun ji cewa ana zaman dar-dar a cocin Dunamis da ke Lugbe Abuja bayan yan sanda da wasu jami'an tsaro masu farin kaya sun zagaye yankin da cocin ya ke saboda tsoron yiwuwar kutsen mambobin #Revolutionnow da ke zanga-zangar kama wasu mambobinsu da DSS suka yi, The Guardian ta ruwaito.

A yayin da The Guardian ta ziyarci cocin a safiyar ranar Lahadi, ta gano yan sanda da dama a yankin, yayin da motoccin sintiri kimanin guda hudu sun tsaya a wasu muhimman wurare a unguwar.

Mai rajjin kare hakkin bil-adama da goyon bayan demokradiyya, Omoyele Sowore, ya yi barazanar sake yin wata gagaruman zanga-zanga idan ba a sako mutane biyar da aka kama sanye da riga mai rubutun 'Buhari Must Go' ba a ranar Lahadi da ta gabata a cocin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164