Ba a fahimce ni bane: Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya nemi afuwa
- Sheikh Abduljabbar ya nemi afuwar al'ummar musulmi game da zargin batanci ga Annabi
- Malamin ya bayyana hakan ne cikin wata sakon murya yana mai cewa ba a fahimce shi bane
- Abduljabbar ya ce idan har ya tabbata cewa abin da ya furta a karatunsa kirkira ya yi toh tabbas yana neman afuwa kuma zai gaggauta tuba
Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya nemi al'ummar musulmi su yi masa afuwa game da kalaman batanci ga Annabi Muhammadu SAW da ake zarginsa da yi yana mai cewa 'ba a fahimce shi' bane, BBC ta ruwaito.
DUBA WANNAN: Ka Yafe Wa Igbobo, Ya Wahala, Ya Gane Kurensa: Basaraken Yarbawa Ya Roƙi Buhari
An ji malaman cikin wani sakon sauti yana cewa:
"Idan har wadannan kalamai daga ni suke, kirkirarsu na yi, ba su a litattafai toh lallai ya isa babban laifi da ya wajaba a gare ni da na gaggauta tuba"
Da Ɗuminsa: Ƴan Bindiga Sun Turo Mana Bidiyon Yadda Suka Aurar Da Ƴaƴanmu Mata, Iyayen Ɗaliban Kebbi
KU KARANTA: Da Ɗuminsa: Ƴan Bindiga Sun Turo Mana Bidiyon Yadda Suka Aurar Da Ƴaƴanmu Mata, Iyayen Ɗaliban Kebbi
Ya cigaba da cewa:
"Amma idan ba daga ni ba ne, daga cikin waɗancen litattafai ne, to wannan kuma ya zama wani abu daban. Sai mu yi rokon Allah ya haska wa al'umma su tashi tsaye mu taimaki addininmu, mu fitar da hadisan karya daga ciki domin gudun kar a rusa mana addinin da su."
A hirar da ya yi da BBC, Abduljabbar ya jadada cewa yana neman afuwar wadanda ke ganin kalaman da ake cewa ya yi suna batanci ne ga Annabi a wajen fassara hadisan da aka gabatar a wurin mukabala.
Kalaman malamin har yanzu na nuna cewa bai sauya abin da ya fada ba tunda farko.
Su wane Abduljabbar ke neman afuwarsu?
Cikin zantawar da BBC ta yi da shi bayan neman afuwar, Abduljabbar ya nanata cewa yana neman afuwar wadanda suka dauka cewa shi ya kirkiri kalaman batanci ga Annabi domin kokawa da ya dinga yi ne neman a kara masa lokacin jawabi yayin mukabalar.
Illar COVID19: Yadda Magidanta a Najeriya Ke Fama da Hauhawar Farashin Kayan Abinci, Duk da Ƙarancin Kuɗin Shiga
Ya ce gaskiyar lamari, bayan zama da aka yi da shi a jiya wanda ba a bada isashen lokaci ba bai bashi damar warware matsalar ba cikin mintuna 10 ko 20 koda ya ke ya nema amma ba a amince masa ba.
Ya cigaba da bayani cewa bukatar a kara lokaci da ya yi don wareware batun ya saka wasu cewa maganganun babu su a hadisai kawai shine ya kirkire su.
A cewarsa:
"Idan har wasu sun dauka miyagun maganganu irin wadannan da ake taba fiyayyen halitta - wadanda nake yaƙin fahimtar da al'umma cewa hadisai ne jabu - kuma wasu suke zaton cewa ni na yi, to ya wajaba na nemi afuwarsu bisa wannan zato da suke yi na cewa maganata ce.
"In har tawa ce kamar yadda suka dauka, kafin afuwarsu afuwar Allah da mazonsa na ke nema."
'Yan Sanda da Jami’an DSS Sun Yi Wa Cocin Dunamis Ƙawanya a Abuja
A wani labarin daban, kun ji cewa ana zaman dar-dar a cocin Dunamis da ke Lugbe Abuja bayan yan sanda da wasu jami'an tsaro masu farin kaya sun zagaye yankin da cocin ya ke saboda tsoron yiwuwar kutsen mambobin #Revolutionnow da ke zanga-zangar kama wasu mambobinsu da DSS suka yi, The Guardian ta ruwaito.
A yayin da The Guardian ta ziyarci cocin a safiyar ranar Lahadi, ta gano yan sanda da dama a yankin, yayin da motoccin sintiri kimanin guda hudu sun tsaya a wasu muhimman wurare a unguwar.
Mai rajjin kare hakkin bil-adama da goyon bayan demokradiyya, Omoyele Sowore, ya yi barazanar sake yin wata gagaruman zanga-zanga idan ba a sako mutane biyar da aka kama sanye da riga mai rubutun 'Buhari Must Go' ba a ranar Lahadi da ta gabata a cocin.
Asali: Legit.ng