Kotu za ta bada umurni a kamo mata tsohuwar Ministan Nigeria da ake zargi da handame dukiyar al'umma

Kotu za ta bada umurni a kamo mata tsohuwar Ministan Nigeria da ake zargi da handame dukiyar al'umma

  • Alkali ya yi barazanar bada umurnin a kamo mata Sanata Stella Oduah saboda kin zuwa kotu
  • Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ne ta gurfanar da tsohuwar ministan sufurin da wasu mutum takwas kan zargin karkatar da kudade
  • Wannan shine karo na hudu da Stella Oduah ta ki gurfana a kotu domin a fara shari'ar da ake tuhumarta da hadi baki da wasu don karkatar da kudade lokacin tana minista

Wata babban kotu da ke zamanta a Abuja ta yi barazanar bada umurnin a kamo mata Stella Oduah, tsohuwar ministan sufurin jiragen sama saboda cigaba da rashin gurfana a gaban kotu, The Cable ta ruwaito.

The Punch ta ruwaito cewa ana tuhumar Stell Oduah, sanata mai wakiltar Anambra da Arewa ne tare da wasu mutane takwas da laifuka masu alaka da almundahar kudade.

Kotu ta yi barazanar bada umurnin kamo mata tsohuwar Ministan Nigeria da ake zargi da handame dukiyar al'umma
Tsohuwar Ministan Sufurin jiragen sama, Sanata Stella Oduah. Hoto: The Cable
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Daga ƙarshe, an kama wanda ya kitsa kisar gillar da aka yi wa Shugaba Moise

Kara karanta wannan

ICPC: Da za a dawo da kudaden da su Abacha suka wawura, da Najeriya ta huta da cin bashi

Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta na zargin Oduah ta bannatar da kudaden al'umma a lokacin da ta ke aiki a matsayin minista.

Sauran wadanda ake karar sune Gloria Odita, Nwosu Emmanuel Nnamdi, Chukwuma Irene Chinyere, Global Offshore and Marine Ltd, Tip Top Global Resources Ltd, Crystal Television Ltd, Sobora International Ltd da China Civil Engineering Construction Corporation (CCECC) Nigeria Ltd.

Za a gurfanar da su ne kan zargin aikata laifuka 25 masu nasaba da hadin baki, karkatar da kudade da amfani da asusun bankuna na sirri a wata bankin zamani a Nigeria.

A yayin da aka fara zaman kotun, Lauyan EFCC, Hassan Liman ya shaidawa kotu cewa masu shigar da karar a shirye suke su gabatar da hujojinsu a kan wadanda suke zargi. Amma tsohuwar ministan da wanda ake tuhuma na hudu ba su hallarci zaman kotun ba.

KU KARANTA: 'Yan Sanda da Jami’an DSS Sun Yi Wa Cocin Dunamis Ƙawanya a Abuja

Kara karanta wannan

Yadda 'yan gudun hijira suka haifi jarirai sama da 17,000 a sansaninsu na jihar Borno

Sau uku Oduah ta ki gurfana a kotu a baya

Wannan shine karo na hudu da tsohuwar ministan ke kin hallartar zaman kotu da aka so yi tun 9 ga watan Fabrairu, 22 ga watan Fabrairu da 19 da watan Afrilu.

Liman ya ce masu shigar da karar za su gabatar da shaidu 32 yayin shari'ar.

Alkalin kotun, Inyang Ekwo, ya ce zai sake saka sabuwar ranar da za a gurfanar da wadanda ake zargin.

Ekwo ya kuma umurci wadanda ake karar su shiga taitayinsu ya kara da cewa zai bada umurnin a kamo duk wadanda aka yi karar idan ba su bayyana a kotu ba a sabuwar ranar da za a gurfanar da su.

Alkalin ya saka ranar 19 da 20 ga watan Oktoba domin gurfanarwar.

An Kama Fasto Da Wasu Mutum Biyu Da Naira Miliyan 15 Na Kuɗaɗen Jabu a Otel

A wani labarin, Ƴan sanda a jihar Niger sun yi holen wasu mutane uku da ake zargi da mallakar kudaden jabu ƴan dubu-dubu da adadinsu ya kai Naira miliyan 15.8, Guardian NG ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Cikakken Bayani: Bayan Sace Sarkin Kajuru, An Sako Ma'aikatan Lafiya da Aka Sace a Yankin

Wadanda ake zargin sune Fasto Sabastine Dabu, ɗan shekara 48 daga Zuru, jihar Kebbi, Emmanuel Aka Zuwa, ɗan shekara 42 daga ƙauyen Adi, ƙaramar hukumar Buruku, jihar Benue da Umar Mohammed, ɗan shekara 50 daga Pandagori, ƙaramar hukumar Rafi, jihar Niger.

Guardian ta ruwaito cewa yayin holen wadanda ake zargin a hedkwatar yan sanda a Minna, kakakin yan sanda Wasiu Abiodun ya yi bayanin cewa ƴan sandan ƙaramar hukumar Kontagora, jihar Niger ne suka kama su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel