Zamfara: Ba za mu bari abin da ya faru da APC a 2019 ya sake faruwa ba, Yeriman Bakura
- Sanata Sani Yerima, ya ce ba za su bari abinda ya faru da APC ta jihar Zamfara a 2019 ya sake faruwa ba
- Tsohon gwamnan na Zamfara ya ce kundin tsarin mulkin jam'iyyar ya fayyace cewa Gwamna na Shugaban jam'iyya a kowacce jiha
- Don haka ya ce babu wani rikici game da batun ballantana a samu wani matsala da zai janyo wa jam'iyyar rasa kuri'u a kotu
Tsohon gwamnan jihar Zamfara kuma mai neman takarar shugabancin kasa a ƙarƙashin Jam'iyyar All Progressives Congress, APC, Sani Yerima, ya ce masu ruwa da tsaki a siyasar jihar za su haɗa kai don ganin ba a maimaita abin da ya faru a 2019 ba, rahoton Daily Trust.
Kotun koli ta soke kuri'un APC a zaben 2019 a jihar Zamfara don jam'iyyar bata da ikon tsayar da ƴan takara don bata yi zaben fidda gwani ba yadda ya dace.
DUBA WANNAN: 'Yan Sanda da Jami’an DSS Sun Yi Wa Cocin Dunamis Ƙawanya a Abuja
A hirar da ya yi da manema labarai a karshen mako a Abuja, Yerima ya ce babu rikici a jam'iyyar APC ta Zamfara kan shigowar Gwamna Bello Matawalle cikin jam'iyyar, Daily Trust ta ruwaito.
Ya ce tsohon gwamnan jihar, Abdulaziz Yari da Sanata Kabiru Marafa ba su goyi bayan gwamnan ya zama jagoran jam'iyyar a jihar ba amma 'nan gaba za su amince'.
Ya ce:
"Kundin tsarin mulkin APC ya fayyace a fili cewa shugaban kasa ne shugaban APC a Nigeria kuma dukkan gwamnonin jihohi sune shugabanni a jiharsu. Don haka babu rikici kan wannan batun.
"Rikicin da ya faru a 2019 ba zai sake maimaita kansa ba domin a lokacin ba ayi zaben fidda gwani da ya dace ba hakan yasa muka tsinci kan mu a rikici."
KU KARANTA: Da Ɗuminsa: Ƴan Bindiga Sun Turo Mana Bidiyon Yadda Suka Aurar Da Ƴaƴanmu Mata, Iyayen Ɗaliban Kebbi
Yerima ya yi bayanin cewa ya shiga jerin masu neman takarar shugabancin kasa ne a 2023 domin ya cancanta bisa tanadin kundin tsarin mulkin ƙasa na 1999, ya kara da cewa zai janye ne kawai idan jam'iyyar ta mika mulki zuwa kudu.
A bangare guda, jam'iyyar ta APC ta kafa kwamiti mai mambobi uku domin tafiyar da harkokin jam'iyyar a jihar.
Mambobin kwamitin sune Sanata Hassan Mohammed Gusau (Shugaba), Muntari Ahmed Anka (Mataimakin Shugaba) da Farfesa Abdullahi Shinkafi (Sakatare).
Tsohon gwamnan Zamfara ya yi watsi da shawarar gwamnonin kudu, ya ce zai yi takara a 2023
A wani labarin daban, tsohon gwamnan jihar Zamfara kuma jigo a jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Sanata Ahmed Sani Yerima, ya ce zai tsaya takarar shugaban kasa a shekarar 2023 duk da matsayar da kungiyar gwamnonin kudu suka dauka a baya-bayan nan.
Kungiyar a ranar Litinin, 5 ga watan Yuli, ta nace cewa ya kamata a mika shugabancin kasar ga yankin Kudancin Najeriya a 2023.
Yayin da yake magana a Abuja tare da wasu ‘yan jarida, Sanata Sani ya ce ba zai yi watsi da kudirinsa ba tunda babu wani tanadi na mulkin karba-karba a kundin tsarin mulkin Najeriya da kuma kudin tsarin mulkin jam’iyyar APC.
Asali: Legit.ng