Na janye kalamaina: Abduljabbar ya amince malaman Kano sun yi nasara a kansa

Na janye kalamaina: Abduljabbar ya amince malaman Kano sun yi nasara a kansa

  • Bayan kai ruwa rana da Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara, shehin malamin ya ce ya janye kalamansa
  • Ya bayyana cewa, yana kuma fatan hakan shi ne silar gafara da rahama a gareshi da kuma shiriya
  • Malamin ya bayyana haka ne bayan da ya nemi gafarar cewa, a baya wasu da dama basu fahimce shi ba

Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya bayyana cewa, a yi masa afuwa kuma lallai ya janey maganganun da ya yi game Manzon Allah SAW wadanda ake ganin sun taba mutuncin ma'aiki.

A cikin wani sauti karo na biyu da ya aike wa sashen Hausa na BBC ranar Lahadi, malamin ya ce yana fatan "hakan ya zama silar gafara da rahama da jin kai gare ni".

KARANTA WANNAN: Da Duminsa: Bayan Sace Sarkin Kajuru, An Sako Ma'aikatan Lafiya da Aka Sace a Yankin

Sheikh Abduljabbar ya ce ya janye dukkan kalamansa game da Annabi Muhammadu SAW
Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara | Hoto: bbc.com/hausa
Asali: Facebook

Ya kara da cewa:

"Wadannan maganganu da suka fito daga bakina suka jawo ce-ce-ku-ce game da Ma'aiki SAW, na janye su na kuma janye su."

Kara karanta wannan

Ba a fahimce ni bane: Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya nemi afuwa

Wannan na zuwa ne 'yan awanni bayan sautin farko da ya fitar a Lahadin yana neman afuwar wadanda suka fahimci cewa shi ne ya kirkiri kalaman batanci ga Annabi da ake zarginsa da yi.

A baya ya ce mutane ne basu fahimce shi ba

A cikin sakon na farko ya ce:

"Idan har wadannan kalamai daga ni suke, kirkirarsu na yi, babu su a litattafai to lallai ya isa babban laifi da ya wajaba a gare ni na gaggauta tuba".

Ya kara da cewa:

"Amma idan ba daga ni ba ne, daga cikin wadancan litattafai ne, to wannan kuma ya zama wani abu daban. Sai mu yi rokon Allah ya haska wa al'umma su tashi tsaye mu taimaki addininmu, mu fitar da hadisan karya daga ciki domin gudun kar a rusa mana addinin da su."

Jawabin nasa na biyu na nuni da cewa ya janye kalaman nasa baki daya ba kamar na farko ba inda yake cewa ya nemi afuwar wadanda ba su fahimce shi ba kadai.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shahararren mawaƙin Nigeria, Sound Sultan ya mutu

An tattaro cewa shehin malamin ya nemi afuwar ce bayan wasu dalibansa sun nemi ya yi hakan.

KARANTA WANNAN: Karin bayani: Yadda 'yan bindiga suka sace shugaban wata kwaleji a jihar Zamfara

Daga Karshe: An Sanya Ranar Mukabala Tsakanin Abduljabbar Kabara da Malaman Kano

A wani labarin, Gwamnatin jihar Kano ta sanya ranar da za a caccaka mukabala tsakanin fitaccen malamin nan Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara da wasu malamai a jihar.

Kwamishinan harkokin addinai na jihar Muhammad Tahir Adamu wanda ake kira Baba Impossible ne ya bayyana haka ranar Alhamis a tattaunawarsa da sashen Hausa na BBC.

Ya ce za a gudanar da mukabalar ce ranar Asabar 10 ga watan Yuli a Hukumar Shari'a dake birnin na Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel