An bankado: Duk da tace ta bar siyasa, Onochie ta yi wa APC wallafa a 2020
- Hadimar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Lauretta Onochie ta yi wa APC wallafa a 2020
- A yayin tantancewa a gaban majalisar dattawa, Onochie ta sanar da majalisa cewa ta bar siyasa tun 2019
- Amma kuma sai aka bankado wata wallafa da tayi tana sanar da taron jam'iyya a 2020
Lauretta Onochie, hadimar shugaban kasa ta yi wallafa kan APC a watan Augustan 2020 akasin yadda ta yi ikirari a ranar Alhamis yayin da ta bayyana a gaban majalisar dattawa.
A yayin da ta bayyana gaban kwamitin hukumar zabe na majalisar dattawa, Onochie ta yi ikirarin cewa ta bar siyasar bangaranci bayan an sake zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2019.
KU KARANTA: Ta fasu: Magu ya hana bincikar Fintiri da wasu tsoffin gwamnoni 3, Kwamitin Salami
KU KARANTA: Da duminsa: PSC ta hana Magu karin girma, ta bayyana umarnin wanda take jira
Hadimar Buharin a fannin yada labarai ta je tantancewa ne a matsayin kwamishinan INEC daga jihar Delta bayan zabenta da shugaba Buhari yayi a watan Oktoban da ya gabata.
"Na ga korafin da aka dinga yi a kaina amma kuma ni adalci nake tsayawa. Don haka babu wanda ya dace ya ji tsoro. Ni mai bin ka'ida ne kuma wannan dalilin ne yasa ake caccakata," Onochie ta sanar da sanatocin.
Amma dukkan ikirarin da hadimar shugaban kasan tayi ba gaskiya bane.
A ranar 24 ga watan Yunin 2020, Onochie ta ce jam'iyyar APC tana cigaba da habaka tare da girma.
"Tabbas akwai taron e-NEC na APC gobe. Muna cigaba da habaka sosai. Ina godiya ga kowa," ta wallafa.
A lokacin da ta rubuta wannan rahoton, kwamitin ayyuka na jam'iyyar wanda Adams Oshiomhole ke shugabanta an watsa shi inda aka hada kwamitin ayyuka na zababbu.
Hadimar shugaban kasan ta yi wannan wallafar ana gobe watsa kwamitin Oshiomhole.
A wani labari na daban, mai bada shawara ta musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Lauretta Onochie, ta ce ita ba 'yar siyasa bace amma tana bin ka'idojin aikinta ne a komai.
Ta sanar da hakan ne yayin jawabin farko yayin da ake tantanceta a matsayin kwamishinan kasa ta INEC a majalisar dattawa, Daily Trust ta ruwaito.
Ta ce, "Bani da jinin bangaranci. Na ga korafe-korafe daban-daban kan zabena da aka yi ba daga PDP ba kadai, har da wasu 'yan APC."
Asali: Legit.ng