Yadda zamu ceto ‘yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci – Osinbajo
- Mataimakin Shugaban Kasa ya kaddamar da kwamitin da zai aikin fitar da ‘yan Najeriya miliyan 100 daga bakin talauci
- Ya ce aikin da kwamitin zai yi a yanzu ya sha banbam da na baya
- Ya bayar da misali da yadda kasar Bangladesh ta fitar da ‘yan kasar da dama daga kangin talauci
Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa gwamnatin Muhammadu Buhari na shirin fitar da ‘yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci a cikin shekara 10.
Osinbajo na mai cewa shirin ba zai kamar wadanda aka saba yi a baya ba, sai dai na yanzun za a aiki da wata dabara ce mai sauki da tsanaki wacce za ta haifar da sakamakon da ake bukata kamar yadda aka yi alkawari.
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun Osinbajo, Laolu Akande, ya saki, yace mataimakin shugaban kasan ya bayyana hakan ne a Abuja ranar Juma'ah a wajen kaddamar da kwamitin na Rage Talauci na Kasa tare da Kwamitin Gudanar da dabarun Tattalin Arziki wanda aka gudanar a Fadar Shugaban Kasa.
Ya bayyana kwarin gwiwa cewa Kwamitin zai iya samar da bukatar kafa shi cikin sauri, ya kara da cewa:
“Domin kar a yi irin abin da aka saba yi a baya inda ake kafa kwamitoci masu karfi wadanda daga karshe ba su cim ma komai ba, a wannan karon dole ne mu kasance masu karfin niyya sosai game da manufofinmu da kuma yadda za mu cim ma manufofin.”
DUBA NAN: Gwamnatin tarayya ta saki hotunan Fursunonin da suka gudu a Jos
KU DUBA: A tarihin Najeriya, babu gwamnatin ta taba jin kan talakawa irin ta Buhari, Gwamna Masari
Ya tabbatar wa mambobin kwamitin cewa gwamnati za ta yi amfani da wata hanya ta daban kuma mafi inganci wajen aiwatar da shirin kawar da talauci a kasar domin samar da sakamakon da ake muradi, rahoton TheSun.
A cewarsa,
“Ina matukar son mu tunkari batun gaba-gadi kuma yadda ya kamata, tare da la’akarin yadda za mu iya magance dukkan matsalolin tare da mai da hankali kan hakikanin ci gaban kasa.
“Ina bukatar da kar mu yi duba da abin da za mu yi, za a yi rubuce-rubuc masu yawa a takarda, amma amfani da hankali shi ne ke bunkasa tattalin arziki a mafi yawan lokuta.
Abin da sauran kasashe suka yi ke nan. Don haka, ina so mu mayar da hankali kan hikima da azanci don mu sami ci gaba a zahiri. ”
Abinda kasar Bangladesh take yi
Da yake ba da misali da kasar Bangladesh kasar da ta aiwatar da dabarun rage talauci, Osinbajo ya lura da yadda bangaren masana'antun kasar ke da muhimmanci.
“A zahiri Bangladesh na fitar da tufafi fiye da yadda muke fitar da mai zuwa kasashen waje. Kasashen da suka yi nasarar fita daga kangin talauci sun samar da ayyuka da dama ta hanyar masana'antu, kuma sun kirkiro da dabaru tare da kyakkyawar niyyar aiwatar da dabarun.
Asali: Legit.ng