Lada ya isa haka: Bayan shekaru 21 wata shahararriyar sanatar PDP ta sauya sheka zuwa APC

Lada ya isa haka: Bayan shekaru 21 wata shahararriyar sanatar PDP ta sauya sheka zuwa APC

  • Jam’iyyar All Progressives Congress ta samu galaba kan wasu mambobin jam’iyyar Peoples Democratic Party a duk fadin kasar
  • Sanata Grace Bent wacce ta wakilci Adamawa ta Kudu a majalisar dattijai tsakanin 2007 da 2011 ta zama sabuwar mamba a APC
  • Bent a ranar Asabar, 10 ga watan Yuli, ta bayyana cewa ta gaji da jam’iyyar adawar saboda haka wannan ne dalilinta na komawa APC

Guguwar sauya sheka ya ci gaba da addabar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) yayin da Sanata Grace Bent ta koma jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Adamawa.

A cewar jaridar The Nation, Bent fitacciyar ‘yar jam’iyyar adawar ta sauya sheka zuwa jam’iyya mai mulki a hukumance, tana mai cewa ta gaji da jam’iyyar bayan shekaru 21.

KU KARANTA KUMA: Allah Ya kunyata Abduljabbar tun a duniya - Mallam Muhammad Rijiyar Lemo

Lada ya isa haka: Bayan shekaru 21 wata shahararriyar sanatar PDP ta sauya sheka zuwa APC
Sanata Grace Bent ta sauya sheka zuwa jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a hukumance Hoto: Auwal D. Sankara
Asali: Facebook

'Yar majalisar wacce ta wakilci Adamawa ta Kudu tsakanin 2007 da 2011 a karkashin PDP ta bayyana cewa ta yanke shawarar ci gaba da mutanen APC.

Kara karanta wannan

Magoya bayan Buhari ba za su taba barin Tinubu ya zama Shugaban Kasa ba – Lamido

Ta samu tarba a jam’iyyar APC daga tsohon shugaban majalisar dattawa, Ken Nnamani a wurin wani liyafa a ranar Asabar, 10 ga watan Yuli, a Yola a madadin Gwamna Mai Mala Buni, shugaban rikon jam’iyyar APC, Nigerian Tribune ta kara ruwaitowa.

Bikin ya samu halartar gwamnonin jihohin Filato, Kebbi, da Jigawa.

Nnamani ya taya ta murnar zabar sabuwar rayuwa ta siyasa a cikin APC kuma ya ba ta tabbacin za ta samu ‘yanci da adalci a fagen wasa don cikar burinta na siyasa a karkashin jam’iyyar.

KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: Manyan masu ruwa da tsaki na APC sun marawa Sanata Musa baya domin ya zama Shugabansu na kasa

Manyan shugabannin PDP na kudu maso gabas sun koma APC, an saki sunaye

A wani labarin, manyan mambobin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a Abia a ranar Juma’a, 9 ga watan Yuli, sun sanar da sauya shekarsu zuwa jam’iyyar All Progress Congress (APC).

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Manyan masu ruwa da tsaki na APC sun marawa Sanata Musa baya domin ya zama Shugabansu na kasa

Daga cikin wadanda suka sauya sheka zuwa jam’iyya mai mulki harda tsohon dan takarar gwamna na Social Democratic Party (SDP), Honarabul Blessing Nwagba, jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito.

Tsoffin jiga-jigan PDP da suka yanke hukuncin a ranar Juma’a su ne Arch Anagha Mba, Cif Silvanus Nwaji, Barr Chibuike Nwokeukwu (SAN), jaridar Guardian ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel