An harbe wani dan siyasar Najeriya har lahira a wajen taron APC a Lagas

An harbe wani dan siyasar Najeriya har lahira a wajen taron APC a Lagas

  • Najeriya ta rasa daya daga cikin ‘yan siyasanta yayin taron jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Legas a ranar Alhamis, 8 ga watan Yuli
  • Wannan ya faru ne lokacin da kamfen din jam’iyya mai mulki a jihar ya juye ya zama rikici da zubar da jini, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar Samuel Kayode wanda shi ne mataimakin shugaban NURTW
  • Wasu ‘yan daba sun harbe dan jam’iyyar na APC a yayin da ya ke kokarin kare wani abokin aikinsa daga tozarci a yayin taron

Shugabannin kungiyar direbobi na kasa (NURTW) a Legas sun tabbatar da kisan mataimakin shugaban kungiyar, Samuel Kayode (wanda aka fi sani da Ekpo Kinkin).

A cewar Jimoh Buhari, kakakin shugaban kungiyar kwadagon, Musiliu Akinsanya, wasu bata gari ne suka harbe Ekpo a ranar Alhamis, 8 ga watan Yuli.

KU KARANTA KUMA: Fadar Shugaban kasa ta yi hasashen abunda zai faru da PDP a babban zaben 2023

An harbe wani dan siyasar Najeriya har lahira a wajen taron APC a Lagas
Rundunar 'yan sanda a jihar ba ta ba da cikakken bayani game da abin da ya faru ba Hoto: Nigerian Police Force
Asali: Facebook

Buhari ya fadawa jaridar Punch cewa lamarin ya faru ne a yayin taron jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a yankin Agboju na Legas.

'Yan daba sun harbe shi

Ya bayyana cewa 'yan baranda da suka mamaye taron ne suka kashe Ekpo, wanda ya ninka a matsayin dan APC yayin da yake kokarin kare wani dan siyasa daga cutuwa.

Kalaman nasa:

"Yana kare wani dan siyasa, Wale Yusuf, daga tsangwama lokacin da 'yan bindigar suka harbe shi."

Da take nakalto wani dan jam’iyyar APC kan lamarin, Vanguard ta ruwaito:

“Ekpo Kinkin mutum ne mai matukar farin jini a wannan yankin. An harbe shi, daidai a sakatariyar Oriade LCDA, kusa da ofishin 'yan sanda na Agboju.

KU KARANTA KUMA: Da duminsa: A karshe fadar Shugaban kasa ta magantu kan rade-radin yiwa Magu karin girma zuwa AIG

"A lokacin turmutsitsin da harbin ya haifar, an ce an ga mutumin da ake zargi da yin harbin, yana fita kai tsaye daga harabar."

Sai dai kuma, rundunar 'yan sanda a Legas ba ta tabbatar da rahoton ba kuma ba ta ba da cikakken bayani game da lamarin ba.

Wasu Yan Bindiga sunyi Awon Gaba da Wani Jigon Siyasa a Jam'iyyar APC

A wani labarin, wasu yan bindiga da ba'a san ko su waye ba sun yi awon gaba da wani jigon siyasa na jam'iyyar APC, Uba Boris, a cikin ƙwaryar Bauchi, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun ritsa abun harin nasu a kan hanyar CBN kusa da gidan mai na AA Rano da misalin ƙarfe 8:00 na daren ranar Laraba.

Yan bindigan, waɗanda suka kai harin a kan mashin guda biyu, sun buɗe wuta domin tsorata mutanen dake wurin, kamar yadda sahara reporters ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel