Da Ɗuminsa: PDP ta sake rasa ɗan majalisar tarayya bayan ya koma APC
- Jam'iyyar hamayya ta PDP ta sake rasa ɗan majalisar tarayya guda ɗaya bayan ya sauya sheka zuwa APC
- Jonathan Gaza, ɗan majalisar tarayya daga jihar Nasarawa ya ce rabuwar kai a PDP na jiharsa ne yasa ya koma APC
- Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule da tsaffin gwamnonin jihar Tanko Almakura da Abdullahi Adamu sun hallarci majalisar don ganin sauya shekar
Jonathan Gaza, ɗan majalisar wakilai na tarayya, ya fice daga jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ya koma All Progressives Congress, APC, Premium Times ta ruwaito.
Mr Gaza ne ɗan majalisar PDP na ƙarshe daga jihar Nassarawa a majalisar kafin ya koma APC a ranar Laraba.
DUBA WANNAN: Hotunan Ƴan Boko Haram Da Aka Kama Da Magungunan Ƙarfin Maza Da Wasu Kayayyaki a Borno
Premium Times ta ruwaito cewa gwamnan jihar Nassarawa, Abdullahi Sule ya tafi majalisar domin halartar sauya sheƙan.
Gwamnan yana majalisar tare da tsaffin gwamnonin jihar, Tanko Almakura da Abdullahi Adamu, wadanda dukkansu sanatoci ne a yanzu.
A wasikar da kakakin majalisar Femi Gbajabiamila ya karanto, Mr Gaza ya ce rabuwar kai da aka samu a jam'iyyar PDP na jiharsa ne dalilin da yasa ya sauya sheƙan.
Wannan shine ɗan majalisa na biyar cikin wadanda suka fice daga APC suka koma PDP a cikin wannan makon.
A ranar Talata, ƴan majalisar tarayya huɗu daga jihar Zamfara sun sanar da komawarsu APC.
Ba a samu rashin amincewa daga ɓangaren marasa rinjaye ba domin shugaban marasa rinjaye, Ndudi Elumelu da mataimakinsa Toby Okechukwu duk ba su nan a majalisar.
Bidiyon Dala: Kotu Ta Umurci Ganduje Ya Biya Ja’afar Ja’afar Tara Bayan Janye Ƙara
A wani labarin daban, wata babban kotun jihar Kano, a ranar Talata ta ci gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje tarar N800,000 bayan ya janye karar bata suna da ya shigar kan mawallafin jaridar intanet ta Daily Nigerian, Daily Trust ta ruwaito.
Ganduje ya maka mawallafin Ja'afar Ja'afar a kotu be saboda labari da bidiyon da ya wallafa inda aka gano wani da aka shine ke saka kudaden kasashen waje a cikin aljihunsa.
Kotun, karkashin jagorancin Mai shari'a Suleiman Danmallan, wadda ta amince da dakatar da shari'ar, ta umurci gwamnan ya biya Ja'afar Ja'afar da kamfaninsa na jaridar N400,000 kowannensu.
Asali: Legit.ng