Na shirya baiwa Fulani filayen kiwo a jihata, Gwamna Ortom

Na shirya baiwa Fulani filayen kiwo a jihata, Gwamna Ortom

  • Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ya sha alwashin baiwa Fulani filin kiwo in har suna bukata a jiharsa
  • Kamar yadda kwamishinan ilimi na jiharsa ya sanar a wani taro da ya wakilci gwamnan, ya ce Ortom na kaunar Fulani
  • Ortom ya jaddada cewa akwai alaka mai kyau tsakanin TIV da Fulani ko a tarihi, don haka zai cigaba da karfafa alakar

Gwamna Samuel Ortom na jihar Binuwai ya ce ba zai yi kasa a guiwa ba wurin ba kowanne bafulatani fili in har yayi niyyar kiwon shanunsa amma a killace.

A yayin jawabi a Abuja a bikin cikar Farfesa Iyorwuese Hagher shekaru 72 a duniya, Ortom ya musanta ikirarin da ake na cewa yana fada da Fulani, Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA: APC ta dawo kamar yadda take da, Buhari yace rikicin jam'iyya ya kare

Na shirya baiwa Fulani filayen kiwo a jihata, Gwamna Ortom
Na shirya baiwa Fulani filayen kiwo a jihata, Gwamna Ortom. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Da duminsa: Kungiyar Niger Delta Avengers ta dawo, ta sha alwashin gurgunta tattalin arzikin Najeriya

Ya ce tarihi ya nuna cewa jama'ar jihar na da alaka mai kyau da Fulani. Gwamnan ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta soki dokar hana kiwo a fili ba inda tace kiwo a killace yafi komai amfani.

Ortom ya sanar da hakan ne ta bakin kwamishinansa na ilimi, Dennis Ityavyar, a inda tsoffin abokai suka hadu domin murna, Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce, "Jama'ar Tiv a tarihi suna da alaka mai kyau da Fulani kuma ina son tabbatar muku da cewa wannan kawancen yana nan. A don haka nake jan kunnen masu amfani da siyasa ko ta'addanci wurin yada jita-jita da su daina.

"Mai girma Gwamna Samuel Ortom yayi bayani cewa jama'ar Benue basu tsani Fulani ba, har yau akwai kawance."

A wani labari na daban, kokarin tsige shugaban hukumar yaki da rashawa na jihar Kano, PCAC, Muhuyi Rimingado, ya tsananta sakamakon zargin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da ake na takurawa majalisar jihar kan aiwatar da hakan.

Wasu majiyoyi daga majalisar jihar sun sanar da Daily Nigerian cewa gwamnan yana so yayi amfani da 'yan majalisar wurin korar shugaban hukumar saboda katsalandan da yayi ga lamurran iyalansa.

Akwai wani shiri da gwamna ke yi na tsige Muhuyi. Duk da gwamnan bai sanar da takamaiman laifin Muhuyi ba, yana dai so ne kawai ya tsige shi daga kujerarsa.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel