Da duminsa: Ba'a ga watan Zhul-Hajji a Saudiyya ba, ranar 20 ga Yuli Sallar Layya
- Kotun Kolin Saudiyya ta sanar da ranar Arafah da Sallar Layya
- Wannan ya biyo bayan fita duban watan da akayi ranar Juma'a
- Za'a duba wata a Najeriya ranar Asabar
Rahoton dake shigo mana da duminsa daga kasar Saudiyya na nuna cewa ba'a ga jinjirin watan Zhul-Hijja 1442 ba a fadin kasar.
Haramain Sharifain da Haramain Live sun ruwaito cewa wannan ya biyo bayan fita neman jinjirin watan da masana suka yi da yammacin Juma'a.
Saboda haka, ranar Lahadi, 11 ga Yuli zai zama 1 ga watan Zhul Hijjah kuma ranar 20 Yuli zai zama ranar Babbar Sallah.
Ranakun la'akari:
Ranar 19 ga Yuli (9 ga Zhul Hijjah) - Ranar hawan Arafah ga mahajjata
Ranar 20 ga Yuli (10 ga Zhul-Hujjah) - Ranar Sallah
KU DUBA: Magoya bayan Buhari ba za su taba barin Tinubu ya zama Shugaban Kasa ba – Lamido
DUBA NAN: Mune kurar baya a kowane bangare, kuma ba mu da ilimi: A cewar wata ‘yar Arewa cikin bidiyo
Yadda ya dace Musulmi ya fuskanci kwanaki goma (10) na farkon watan Zhul-Hijja, Daga Sheikh Umar Zaria
Yayinda watan zai fara ranar Lahadi, Malamai sun yi bayani kan muhimmancin kwanaki 10 na farko a wannan wata.
Babban Malami, Sheikh Umar Shehu Zariya, ya yi rubutu da dalilin da yasa aka fifita wadannan ranaku.
Karanta a nan: https://hausa.legit.ng/1424310-yanda-ya-dace-musulmi-ya-fuskanci-kwanaki-goma-10-na-farkon-watan-dhul-hijjah.html
Asali: Legit.ng