Shugaban Hukumar NCFRMI Na Kano, Zeenat Kaltume-Yahaya, Ta Rasu

Shugaban Hukumar NCFRMI Na Kano, Zeenat Kaltume-Yahaya, Ta Rasu

  • Shugaban hukumar kula da yan gudun hijira na Kano, Zeenat Kaltume-Yahaya, ta rasu
  • Kaltume-Yahaya ta rasu ne a jiya Alhamis bayan gajeruwar rashin lafiya a Kano
  • Marigayiyar ta rasu ta bar mijinta, Alhaji Baba Musa Yahaya da yara biyu, Hauwa Yahaya da Muhsin Yahaya

Shugaban hukumar kula da yan gudun hijira da wadanda suka rasa muhallinsu, NCFRMI, na jihar Kano, Mrs Zeenat Kaltume-Yahaya, ta rasu tana da shekaru 48, Daily Nigerian ta ruwaito.

Mai bada shawara na musamman kan kafafen watsa labarai na kwamishinan NCFRMI, Sadiq Abdullateef, wanda ya bada sanarwar a ranar Juma'a, ya ce Kaltume-Yahaya ta rasu a daren Alhamis bayan gajeruwar rashin lafiya.

DUBA WANNAN: Kano: Ɗalibi ya cinnawa kansa wuta saboda bai samu kuɗin biyan jarrabawar NECO ba

Shugaban Hukumar NCFRMI Na Kano, Zeenat Kaltume-Yahaya, Ta Rasu
Shugaban Hukumar NCFRMI Na Kano, Zeenat Kaltume-Yahaya, Ta Rasu. Hoto: Daily Nigerian
Asali: Facebook

Sanarwar ta ce:

"Muna sanar da rasuwar abokiyar aikin mu Zeenat Kaltume Yahaya.
"Hajiya Zeenat ta rasu ne bayan awanni kadan da rashin lafiya a daren jiya a Kano, ta rasu tana da shekaru 48 ta kuma bar mijinta, Alhaji Baba Musa Yahaya da yara biyu, Hauwa Yahaya da Muhsin Yahaya."

Kara karanta wannan

Abdulsalami ya ja kunnen ‘yan siyasa da cewa sauya sheka ka iya haddasa husuma

KU KARANTA: Gwamnatin Katsina za ta wajabtawa kowanne baligi harajin N2000, shanu kuma N500 matsayin Jangali

A sakon ta'aziyyar, kwamishinan dai-daito na NCFRMI, Imaan Sulaiman-Ibrahim, ta bayyana marigayiyar a matsayin ma'aikaciya mai jajircewa wurin aiki.

"Ina addu'ar Allah (SWT) ya jikan ta ya kuma bawa wadanda ta bari a baya hakurin jure rashi."

Sanarwar ta kuma sanar da cewa za a yi wa marigayiya Kaltume-Yahaya jana'iza bisa koyarwa addinin musulunci a ranar Juma'a da safe a Kano.

Sarki mai daraja ta ɗaya a Arewa ya rasu bayan shekaru 45 kan karagar mulki

Sarkin Lafiagi, Mai martaba Alhaji Saadu Kawu Haliru ya riga mu gidan gaskiya kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Rahotanni sun ce basaraken ya rasu ne a wani asibiti a Abuja misalin ƙarfe 6 na yammacin ranar Alhamis.

Wata majiya ta shaidawa Daily Trust cewa za a kai gawarsa jihar Kwara a ranar Juma'a zuwa Lafiagi, ƙaramar hukumar Edu inda za a yi masa jana'iza bisa koyarwar addinin musulunci.

Kara karanta wannan

Ba za mu iya yin galaba kan ‘yan ta’adda ta hanyar amfani da tsofaffin makamai ba: Janar Irabor

Asali: Legit.ng

Online view pixel