AfDB ta nada Barrow a matsayin sabon shugaban ofishinta na Najeriya

AfDB ta nada Barrow a matsayin sabon shugaban ofishinta na Najeriya

  • Bankin Habaka Afrika (AfDB) ta nada Lamin Barrow a matsayin sabon darakta janar din ta na Najeriya
  • Kamar yadda Adesina ya bayyana, gogewar Barrow dan asalin Gambia a harkar diflomasiyya za ta taimaka musu
  • Shugaban AfDB ya bayyana cewa ofishinsu na Najeriya yana da matukar amfani, lamarin da yasa suka saka kwararre shugabanci

Bankin habaka Afrika (AfDB) ya nada Lamin Barrow dan asalin kasar Gambia a matsayin darakta janar na ofishinsu na Najeriya.

A wata takarda da aka fitar, bankin ya ce nadin ya fara aiki daga ranar 1 ga watan Yulin 2021.

Lokacin da Barrow ya fara aiki da AfDB

Barrow ya fara aiki a bankin a 2000 kuma shine mukaddashin babban darakta na ofishinsu na Najeriya kafin a yi masa wannan nadin, Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA: Fitaccen jarumin fina-finan Indiya, Dilip Kumar ya riga mu gidan gaskiya

AfDB ta nada Barrow a matsayin sabon shugaban ofishinta na Najeriya
AfDB ta nada Barrow a matsayin sabon shugaban ofishinta na Najeriya. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan Boko Haram sun bindige mutum 18 a Adamawa

Barrow ya mika godiya ga Adesina

A yayin tsokaci kan nadin da aka masa, Barrow ya ce, "Ina matukar godiya ga shugaba Adesina kan wannan nadin wanda ya samar min da babbar dama ta bada gudumawata."

Yana da digirin digir a fannin tsumi da tattali daga jami'ar Boston dake USA inda yake da digirinsa na farko daga jami'ar Najeriya dake Ibadan, TheCable ta ruwaito.

Shugaba Adesina yayi bayanin hikimar nadin

A yayin tsokaci kan wannan nadin, Dr. Akinwumi Adesina, shugaban AfDB ya ce, "Ofishinmu na kasar Najeriya yana da matukar amfani domin shi ke kula da yawancin ayyukanmu tare da gwamnatocin jihohi da kuma bangarori masu zaman kansu.

"Gogewar Lamin a bangaren shugabanci, iliminsa na fannin aiki da kuma kwarewarsa a bangaren diflomasiyyya da alaka da gwamnati zai taimaka wurin fadada ayyukanmu tare da inganta alakarmu da gwamnati da sauran wadanda muke hulda dasu a Najeriya."

A wani labari na daban, Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya sake yin kira da a mika mulki yankin kudancin kasar nan inda ya goyi bayan zauren gwamnonin kudanci a matsayarsu ta zaben yankin da zai yi shugabancin kasa a 2023.

A wani taro da gwamnonin kudancin suka yi a Legas a ranar Litinin, sun aminta da cewa yankinsa ne ya dace ya fitar da shugaban kasa na gaba idan za a duba adalci da daidaito, lamarin da Zulum ya bada goyon baya.

"Na fadi ba sau daya ba ko biyu, Ni Farfesa Babagana Zulum, na tsaya a matsayar cewa a mika shugabancin kasa zuwa yankin kudu a 2023 saboda hadin kan kasar nan yana da amfani," gwamnan ya sanar a wata tattaunawa da aka yi da shi a Channels TV a shirin gari ya waye na ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Online view pixel