Da dumi-dumi: Shugaba Buhari ya yi sabon nadi mai muhimmanci
- Shugaba Buhari ya amince da nadin Adamu Mohammed Abdulhamid a matsayin jakadan Najeriya a Kungiyar Kasuwanci ta Duniya
- An tattaro cewa nadin nasa zai shafe tsawon shekaru hudu
- Abdulhamid ya kasance jagoran yakin neman zaben Ngozi Okonjo-Iweala a Geneva wanda ya taimaka kwarai da gaske wajen zamantowarta babbar darakta ta WTO
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Adamu Mohammed Abdulhamid a matsayin jakadan Najeriya a Kungiyar Kasuwanci ta Duniya (WTO).
An sanar da sabon nadin da aka yiwa Abdulhamid, wanda zai shafe tsawon shekaru hudu, a cikin wata wasika daga ofishin shugaban ma’aikatan Shugaba Buhari, Ibrahim Gambari, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.
KU KARANTA KUMA: Kaduna: CP ya bayyana yadda ‘yan bindiga suka farma makarantu 5, suka sace dalibai 204 a cikin watanni shida
Kafin sabon nadin nasa, Abdulhamid ya yi aiki a matsayin Shugaban riko / mai kula da harkokin Ofishin Kasuwancin Najeriya a WTO, Geneva, Switzerland.
Waiwaye: Bidiyon Shagari yana kunna sigari lokacin da Firayim Minista Tafawa Balewa ke jawabi ga taron jama'a
Ya kuma kasance jagoran yakin neman zaben Ngozi Okonjo-Iweala a Geneva wanda ya taimaka kwarai da gaske wajen zamantowarta babbar darakta ta WTO.
KU KARANTA KUMA: An harbe wani dan siyasar Najeriya har lahira a wajen taron APC a Lagas
Jakadan ya sami MSC a fannin Tattalin Arziki da Ci Gaban Kasa da Kasa daga Jami'ar Clemont Ferrand, Faransa, ya yi digirinsa na biyu a kan Gudanar da Harkokin Kasuwanci da Shugabanci daga Makarantar London Graduate School, Burtaniya; takardar shaida na alaƙar ƙasa da diflomasiyyar tattalin arziki daga Jami'ar Commonwealth, Landan.
Kungiyoyin mata sun kai karar Buhari a kotu, sun ce gwamnatin tarayya ta ware su a gefe
A wani labarin, jaridar Punch ta ce gamayyar kungiyoyin mata sun shigar da karar gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari a gaban wani kotun tarayya a Abuja.
Kungiyoyin su na ikirarin cewa gwamnatin da Muhammadu Buhari yake jagoranta, ba ta yi da mata.
A wannan kara da kungiyoyin suka shigar, sun bukaci kotu ta hana shugaban Najeriyar cigaba da saba ka’idar da ta ce a ba mata 35% na mukaman gwamnati.
Asali: Legit.ng