Kaduna: CP ya bayyana yadda ‘yan bindiga suka farma makarantu 5, suka sace dalibai 204 a cikin watanni shida

Kaduna: CP ya bayyana yadda ‘yan bindiga suka farma makarantu 5, suka sace dalibai 204 a cikin watanni shida

  • Kwamishinan 'yan sandan jihar Kaduna, Umar Muri, ya yi bayani dalla-dalla kan hare-haren' yan ta'addan da suka faru a Kaduna cikin watanni shida
  • Muri ya bayyana hakan ne yayin ganawa da Sufeta-Janar na 'yan sanda (IGP), Usman Alkali Baba a Kaduna
  • Kwamishinan ya bayyana cewa rundunar jihar na fuskantar matsalolin da suka hada da satar mutane da fashi da makami

Umar Muri, kwamishinan ‘yan sandan jihar Kaduna, ya bayyana cewa ‘yan fashi sun sace dalibai 204 daga watan Janairun 2021 zuwa yau a cikin jihar.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 8 ga watan Yuli, yayin da yake yiwa Sufeto Janar na ‘yan sanda (IGP), Alkali Baba Usman, bayani a Kaduna.

KU KARANTA KUMA: An harbe wani dan siyasar Najeriya har lahira a wajen taron APC a Lagas

Kaduna: CP ya bayyana yadda ‘yan bindiga suka farma makarantu 5, suka sace dalibai 204 a cikin watanni shida
An sanar da Sufeto-Janar na 'yan sanda (IGP) Usman Baba game da ayyukan' yan fashi a jihar Kaduna Hoto: Nigeria Police.
Asali: Twitter

Legit.ng ta tattaro cewa Muri ya lura da cewa rundunar ta gamu da matsalolin aikata laifuka da suka hada da satar mutane, fashi da makami, satar shanu, fataucin mutane da sauran kananan laifuka.

Satar yaran makaranta abun bacin rai da dabbanci ne

Ya sanar da IGP cewa babban laifin da ya addabi jihar shi ne rashin tuba da mummunan ayyukan masu satar mutane na sace dalibai daga makarantun koyon karatu da wasu hanyoyi.

A cewarsa, hanyoyin sun hada da babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja, hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari da hanyar Kaduna zuwa Zariya.

Muri ya ce:

“Daga bayanan da muka samu, makarantun da aka kaiwa hari da kuma sace daliban da aka yi a jihar Kaduna daga watan Janairun 2021 zuwa yau kadai sun hada da Kwalejin Gandun Daji, Mando Afaka –inda aka sace dalibai talatin da bakwai (37) a ranar 11 ga Maris, 2021, kuma daga baya an kubutar da su."

Ya ce an samu lamuran satar mutane biyu a kwalejin fasaha ta Nuhu Bamalli, Zariya, ya kara da cewa na farko da ya kunshi dalibai uku (3) a ranar 14 ga Disamba, 2020.

Muri ya kara da cewa daga baya ne wadanda suka sace su suka sake su, ya kara da cewa an sake samun lamarin na biyu a ranar 10 ga Yuni, wanda ya hada da malamai biyu (2) da dalibai bakwai (7).

An sako dalibai da malaman da aka sace a Nuhu Bamalli Poly

A wani labarin, an sako dalibai shida da malamai biyu da yan bindiga suka sace a kwalejin fasahar Nuhu Bamalli dake Zariya jihar Kaduna kwanakin baya.

ChannelsTV ta rahoto cewa an sakesu ne da daren Alhamis.

Kakakin kwalejin fasahar, Abdullahi Shehu, wanda ya tabbatar da rahoton yace dalibai da malaman sun samu yanci ne bayan tattaunawa tsakanin 'yan uwansu da yan bindigan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel