Kungiyoyin mata sun kai karar Buhari a kotu, sun ce gwamnatin tarayya ta ware su a gefe

Kungiyoyin mata sun kai karar Buhari a kotu, sun ce gwamnatin tarayya ta ware su a gefe

  • Wasu kungiyoyi da ke kare hakkin mata sun yi karar gwamnatin tarayya a kotu
  • Wadannan kungiyoyin sun ce shugaba Muhammadu Buhari ba ya tafiya da su
  • An daga shari’ar zuwa karshen watan Satumba domin Lauyoyi su shirya a kotu

Jaridar Punch ta ce gamayyar kungiyoyin mata sun shigar da karar gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari a gaban wani kotun tarayya a Abuja.

Kungiyoyin su na ikirarin cewa gwamnatin da Muhammadu Buhari yake jagoranta, ba ta yi da mata.

A wannan kara da kungiyoyin suka shigar, sun bukaci kotu ta hana shugaban Najeriyar cigaba da saba ka’idar da ta ce a ba mata 35% na mukaman gwamnati.

KU KARANTA: Majalisa ta tantance Hadimar Buhari da ake so a ba mukami

Wadannan kungiyoyi na mata sun ce kin ba mata akalla 35% na kujerun gwamnatin tarayya ya saba kundin tsarin mulki da ka’idar jinsi na shekarar 2006.

Jaridar ta ce kungiyoyin sun ce ware su da aka yi, ya saba wa tsarin kare hakkin Bil Adama na Afrika.

Har ila yau wadannan masu kare hakkin mata sun zargi gwamnatin tarayya da watsi da dokar kasa wajen kin ba mata mukamai da kuma kujeru masu tsoka.

An shigar da kara a kotu, an soma shari'a

Marshal Abubakar shi ne lauyan da ya shigar da wannan kara a gaban Alkali Donatus Okorowo. Ibukun Okoosi shi ne lauyan da ya ke kare wadanda ake tuhuma.

Muhammadu Buhari da iyalinsa
Muhammadu Buhari, Aisha-Buhari da 'Ya 'yansa
Asali: Facebook

KU KARANTA: Kwamitin da aka kafa domin ya zauna da Twitter bai soma aiki ba

A zaman da aka yi na ranar Alhamis, 8 ga watan Yuli, 2021, Alkali mai shari’a, Donatus Okorowo, ya dage karar zuwa ranar 29 ga watan Satumban shekarar bana.

All Africa ta ce an hada da Ministan shari’a na tarayya, Abubakar Malami SAN a wannan shari’a.

Kungiyoyin da su ka kai karar Gwamnati

Kungiyoyin da su ka shigar da wannan kara su ne: Empowerment and Legal Aid Initiative, da Women Trust Fund, da Centre for Democracy and Development.

Sai kuma West Africa Women Advocates Research and Documentary Centre, da Vision Spring Initiative, da kuma kungiyar nan ta Women in Politics ta Najeriya.

Kun samu labari cewa ‘Yan bindiga sun yi awon-gaba da mutum akalla 15 a garin Kaduna, sun nemi a biya Naira miliyan 150 kafin a fito da su.

Miyagun ‘Yan bindiga sun sake dura jihar Kaduna, sun yi garkuwa da mutane bayan an shiga wata makarantar addini da ke yankin Chikun.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng