Wasu Yan Bindiga sunyi Awon Gaba da Wani Jigon Siyasa a Jam'iyyar APC

Wasu Yan Bindiga sunyi Awon Gaba da Wani Jigon Siyasa a Jam'iyyar APC

  • Yan bindiga sun ɗauke wani babban ɗan siyasa kuma ɗan jam'iyyar APC a jihar Bauchi
  • Wani shaida yace maharan sun buɗe wuta domin tsorata mutanen dake wurin kafin su yi awon gaba da abin harin su
  • Har yanzun ba'a gano inda yan bindigan suka yi da ɗan siyasan ba, kuma basu nemi kowa ba

Wasu yan bindiga da ba'a san ko su waye ba sun yi awon gaba da wani jigon siyasa na jam'iyyar APC, Uba Boris, a cikin ƙwaryar Bauchi, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Yanzu-Yanzu: Yan Boko Haram Sun Kai Hari Jihar Yobe da Motocin Yaƙi

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun ritsa abun harin nasu a kan hanyar CBN kusa da gidan mai na AA Rano da misalim ƙarfe 8:00 na daren ranar Laraba.

Yan bindigan, waɗanda suka kai harin a kan mashin guda biyu, sun buɗe wuta domin tsorata mutanen dake wurin, kamar yadda sahara reporters ta ruwaito.

Yan bindida sun sace ɗan siyasa a Bauchi
Wasu Yan Bindiga Yi Awon Gaba da Wani Jigon Siyasa a Jam'iyyar APC Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa mutanen sun fito da ɗan siyasan daga motarsa zuwa wata mota, daga bisa ni suka yi awon gaba da shi.

Yace: "Maharan sun tilasta masa fitowa daga motarsa zuwa wata mota dake ajiye a gefe, daga nan suka tafi da shi ba tare da sun daina harba bindiga sama ba."

"Da farko sun bi hanyar zuwa Nasarawa, amma sai suka juyo saboda sun hangi motar sintiri ta yan sanda."

KARANTA ANAN: Karin Bayani: Yan Bindiga Sun Sake Yin Awon Gaba da Aƙalla Mutum 13 a Kaduna

Har yanzun babu labari dangane da dan siyasan

Har zuwa safiyar Alhamis ba'a san inda jigon APC yake ba, kuma ɓarayin basu tuntuɓi kowa ba don neman kuɗin fansa.

Kakakin hukumar yan sanda ta jihar Bauchi, SP Mohammed Ahmed Wakili, bai fitar da wata sanar wa dangane da sace Mr. Boris ba.

A wani labarin kuma Ma'aikata 774,000: FG Ta Bayyana Abinda Take Shiryawa Ma'aikatan SPW Bayan Gama Biyansu N60,000

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa zata shirya wa ma'aikatan SPW horo na musamman a kan ƙananan sana'o'i.

Gwamnatin tace zata shirya wannan bayad da horon ne a kowace mazaɓar sanata dake faɗin ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel