Bidiyon yadda iyaye suka dungi kuka yayin da suka isa makarantar da ‘yan bindiga suka sace dalibai a Kaduna

Bidiyon yadda iyaye suka dungi kuka yayin da suka isa makarantar da ‘yan bindiga suka sace dalibai a Kaduna

  • Wasu iyayen daliban da ake zargin 'yan fashi sun sace a wata makaranta a jihar Kaduna sun kasa daina kuka
  • Bidiyo ya nuno iyayen da ke cikin bakin ciki yayin da Najeriya ke ci gaba da fama da matsalar rashin tsaro da matsalolin garkuwa da mutane
  • Wasu da ake zargi ‘yan fashi ne sun afkawa makarantar sakandaren Betel Baptist da ke garin Damishi na Chikun a safiyar ranar Litinin, 5 ga watan Yuli

An yi kuka a Kaduna bayan wasu da ake zargin 'yan fashi ne sun sace wasu daliban da ba a tantance adadinsu ba na makarantar sakandaren Betel Baptist da ke garin Damishi na karamar hukumar Chikun na jihar a ranar Litinin, 5 ga watan Yuli.

A cikin bidiyo masu sosa rai wanda shahararren dan jaridar nan Babajide Kolade-otitoju ya yada a Facebook, an ga wasu daga cikin iyayen daliban da aka sace suna ta kuka ba kakkautawa.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An yi harbe-harbe yayin da aka dakatar da shugaban marasa rinjaye da wasu ‘yan majalisar Imo 5

Bidiyon yadda iyaye suka dungi kuka yayin da suka isa makarantar da ‘yan bindiga suka sace dalibai a Kaduna
Wasu daga cikin iyayen daliban da ‘yan bindiga suka sace a Kaduna Hoto: Babajide Kolade-otitoju
Asali: Facebook

Shugaban kungiyar kiristocin Najeriya (CAN) reshen jihar, Rev. John Hayab, ya ce har zuwa ranar Juma'a, akwai daliban kwana 180 a makarantar.

A cewarsa, dalibai 26 sun dawo kuma yana da kwarin gwiwar cewa wasu da yawa za su tsere daga hannun 'yan fashin.

'Yan Najeriya sun yi martani kan lamarin

Da yake maida martani, Ajayi Taiwo Oluwole ya ce:

"Babajide Kolade-otitoju Ina ganin lokaci ya yi da ya kamata duk makarantar kwana a Kaduna ta rufe sannan dalibai su dunga zuwa makaranta da rana kawai. 11:00 am-3:00 pm."

Abigail Dada Auta tayi sharhi:

"Don Allah, ya kamata Gwamnatin Jiha ta rufe duk makarantun da ke kaduna."

Afolabi Daniel ya rubuta:

"Ya kamata gwaminati ta rufe makarantu a Kaduna har sai abin da hali yayi."

Efemena Edafioka ya ce:

"Najeriya daya. Wannan Gwamnatin ta ji kunya. Na koka ma wannan tawayen da ake kira Najeriya. Dokoki iri daya amma aiki daban."

Yan Bindigan da Suka Sace Ɗalibai a Kaduna Sun Yi Watsi da Buhun Shinkafa 9 da Aka Kai Musu

A wani labari, yan bindigan da suka sace ɗalibai a makarantar sakandire ta Bethel Baptist, sun yi watsi da buhunan shinkafa 9 da sauran kayan abinci da hukumar makarantar ta kai musu, kamar yadda punch ta ruwaito.

Mataimakin shugaban makarantar, Wakili Madugu, shine ya bayyana haka a wata fira da yayi da gidan radiyon 'Nigerian Info Abuja' ranar Alhamis.

Madugu, yace maharan sun kira shi a waya da misalin ƙarfe 7:30 na safe ranar Talata, sun tabbatar da cewa yaran suna cikin ƙoshin Lafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel