Karin Bayani: Jerin Sunayen Sabbin Shugabannin Jami'o'in FG da Shugaba Buhari Ya Naɗa

Karin Bayani: Jerin Sunayen Sabbin Shugabannin Jami'o'in FG da Shugaba Buhari Ya Naɗa

  • Shugaba Buhari ya naɗa tsohon shugaban hukumar INEC, Farfesa Jega, a matsayin shugaban majalisar gudanarwa na UniJos
  • Wannan na ƙunshe ne a wani jawabi da ministan Ilimi, Adamu Adamu, yayi wa manema labarai a Abuja
  • Hakanan, Buhari ya naɗa sabbin shugabannin jami'o'in tarayya, waɗanda mafi yawancin su sarakuna ne

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya amince da naɗin tsohon shugaban hukumar zaɓe, INEC, Farfesa Attahiru Jega, a matsayin shugaban majalisar gudanarwa na jam'iar Jos (UNIJOS), kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Ma'aikata 774,000: FG Ta Bayyana Abinda Take Shiryawa Ma'aikatan SPW Bayan Gama Biyansu N60,000

Ministan ilimi, Adamu Adamu, wanda ya bayyana haka ga manema labarai a Abuja, yace Buhari ya amince da naɗin shugabannin jami'o'in tarayya 42 dake faɗin ƙasar nan, kamar yadda daily nigerian ta ruwaito.

Shugaban ya kuma amince da naɗin biyu daga cikin tsofaffin ministocinsa, Prof Anthony Anwuka da Udoma Udo Udoma, a matsayin shugabannin majalisar zartarwa a wasu jami'o'i.

Farfesa Attahiru Jega
Da Ɗumi-Ɗumi: Shugaba Buhari Ya Naɗa Tsohon Shugaban INEC, Attahiru Jega, a Sabon Muƙami Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Yayinda da Anwuku zai jagoranci majalisar jami'ar albarkatun man fetur dake Effurum, jihar Delta, shi kuma Udoma zai jagoranci ta jami'ar Bayero dake Kano.

Buhari ya naɗa shugabannin jami'o'in tarayya

Hakanan kuma shugaba Buhari ya amince da naɗin shugabannin jami'o'i (Chancellors) mallakin gwamnatin tarayya.

Adamu, yace: "Kamar yadda mukasan iyayen mu sarakuna suke yi, muna fatan waɗannan shugabannin su zama masu kyautatawa jami'ar da aka tura su."

"An ɗauke su daga yankin da suke gudanar da mulkinsu zuwa wani wuri na daban kuma muna fatan waɗannan naɗe-naɗen zasu taka rawa wurin ƙara danƙon zumunci tsakanin al'ummar Najeriya."

Jerin sunayen sabbin shugabannin jami'o'i da inda aka tura su

Jami'ar Benin- HRM Prof James Ortese Iorzua Ayatse.

Jami'ar Abubakar Tafawa Ɓalewa, Bauchi- Oba Rufus Adeyemo Adejugbe Aladesanmi III.

Jami'ar Ahmaɗu Bello Zaria, jihar Kaduna- HM Obi Ofala Nnaemeka Alfred Achebe.

Jami'ar Alex Ekwueme daje Ndufu-Alike, jihar Ebonyi- HRM Oba Aremu Gbadebo.

Jami'ar Bayero Kano-HM, Oba Ewuare 11, Basaraken Benin.

Jami'ar gwamnatin tarayya dake Dutse, jihar Jigawa- HRM Sarki W S Joshua Igbugburu X, Con, Ibenanawei na masarautar Bomo.

Jami'ar gwamnatin tarayya daje Gashua- HRM Farfesa Joseph Chike Edozien. CFR, Sarkin Asaba.

Jami'ar tarayya Lokoja, jihar Kogi- HRH Alhaji (Dr.) Mohammadu Abali Ibn Mohammed Idris, CON, Sarkin Fika.

Jami'ar tarayya Dutsin-ma, jihar Katsina- Sarki Dandeson Douglas Jaja Jeki, Amanyanabo na masarautar Opobo.

Jami'ar Michael Okpara, Umuduke- HRH Alhaji Abubakar Shehu Abubakar III, Sarkin Gombe.

KARANTA ANAN: Yanzu-Yanzu: Yan Boko Haram Sun Kai Hari Jihar Yobe da Motocin Yaƙi

Ministan ya ƙara da cewa za'a gabatar da sabbin shugabannin ga jami'arsu a bikin yaye ɗalibai na kowace makaranta nan gaba.

Jami'ar tarayya dake Otuoke. jihar Bayelsa- HRH, Justice Sidi Bage Muhammad 1, Sarkin Lafia.

A wani labarin kuma Rikicin Siyasa: Jam'iyyar APC Ta Gayyaci Ministan Buhari Kan Wani Zargi

Jam'iyyar APC ta ƙasa ta aike da takardar gayyata ga ministan yaɗa labarai da al'adu, Alhaji Lai Muhammed.

APC ta gayyaci ministan ne ya zo ya mata bayani kan dalilin buɗe wata sabuwar sakateriya a jihar Kwara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262