Yanzu Yanzu: An yi harbe-harbe yayin da aka dakatar da shugaban marasa rinjaye da wasu ‘yan majalisar Imo 5

Yanzu Yanzu: An yi harbe-harbe yayin da aka dakatar da shugaban marasa rinjaye da wasu ‘yan majalisar Imo 5

  • An samu hargitsi a majalisar dokokin jihar Imo bayan dakatar da shugaban marasa rinjaye da wasu ‘yan majalisa biyar da aka yi
  • Kakakin majalisar, Paul Emezim ne ya tsige ‘yan majalisar a wani taron gaggawa da aka kira a yau Alhamis, 8 ga watan Yuli
  • Lamarin ya kai ga har said a aka yi harbe-harbe a harabar majalisar yayin da aka gudanar da zanga-zanga

Wani rahoto da jaridar The Punch ta fitar ya nuna cewa an samu hayaniya a harabar majalisar dokokin jihar Imo a Owerri, babban birnin jihar, a ranar Alhamis, 8 ga watan Yuli.

Legit.ng ta tattaro cewa tashin hankalin ya biyo bayan dakatar da shugaban marasa rinjaye, Anyadike Nwosu, da wasu ‘yan majalisa biyar da kakakin majalisar, Paul Emezim yayi.

KU KARANTA KUMA: Sadu da yaron da ya fara koyon yadda ake tuka jirgi a shekara 7

Yanzu Yanzu: An yi harbe-harbe yayin da aka dakatar da shugaban marasa rinjaye da wasu ‘yan majalisar Imo 5
An dakatar da shugaban marasa rinjaye da wasu ‘yan majalisar Imo biyar Hoto: Hope Uzodinma.
Asali: Facebook

A wani zama na gaggawa da aka gudanar karkashin tsauraran matakan tsaro, kakakin majalisar ya dakatar da ‘yan majalisar har sai baba-ta-gani saboda abin da ya kira “dabi’un da ba na majalisa ba."

Kakakin majalisar ya kuma dakatar da tsohon shugaban masu rinjaye nan take, Uche Ogbuagu, (Ikeduru, APC), Onyemaechi Njoku (Ihitte- Uboma, APC), Kennedy Ibeh, (Obowo, APC), Philip Ejiogu, (Owerri ta Arewa, PDP) da Dominic Ezerioha (Oru West, APC).

Shugaban majalisar Emezim ya rusa kwamitin majalisar dokokin Imo

Jaridar The Nation ta kuma ruwaito cewa Emezim ya rusa dukkanin kwamitocin majalisar ya kuma tsige bulaliyar majalisar, Authur Egwim, (Ideato ta Arewa, APC) sannan ya maye gurbinsa da Obinna Okwara (Nkwerre, APC).

Wannan lamarin ya haifar da firgici a cikin harabar yayin da masu taimaka wa shugaban majalisar kan tsaro suka yi harbi a sama tare da kare Emezim, don ya samu hanyar fita daga harabar, yayin zanga-zanga.

Daya daga cikin ‘yan majalisar da aka dakatar, Ibeh ya shaida wa majiyarmu cewa:

“Mun samu sako a yau daga magatakardan majalisar cewa za a yi taron gaggawa a yau (Alhamis) kasancewar a ranar Laraba an dage zaman har zuwa 14 ga watan Yuli.

KU KARANTA KUMA: Da Ɗumi-Ɗumi: Shugaba Buhari Ya Naɗa Tsohon Shugaban INEC, Attahiru Jega, a Sabon Muƙami

“Mun isa zauren da karfe 10 na safe amma ba mu ga kakakin ba. Mun ci gaba da jira har sai lokacin da kakakin ya zo kuma muka shiga cikin zauren sannan kuma muka sanya hannu kan rajistar halartar zama. Shugaban majalisar nan take ba tare da komawa ga dokokin majalisar ba ya ba da sanarwar rusa dukkanin kwamitocin majalisar tare da tsige bulaliyar majalisar sannan ya sanar da Obinna Okwara, a madadinsa.
“Shugaban majalisar ya ce an yanke shawarar ne a zaman zartarwa na majalisar, alhali babu wani zama na shugabannin majalisar. Wani dan majalisa, Onyemaechi Njoku, ya tashi tsaye kan dokar musamman ta alfarmar majalisar, amma kakakin majalisar ya share shi. Nima na tashi yin magana amma bai bar ni in yi magana ba.
“Ya yi watsi da dokokin majalisar ya shigo da nasa. Sauran ‘yan majalisar sun ja hankali amma kakakin majalisar bai damu ba. A karshe, ya sanar da cewa ya dakatar da mu shidan saboda rashin bin doka.”

A wani labari na daban, Wasu yan bindiga da ba'a san ko su waye ba sun yi awon gaba da wani jigon siyasa na jam'iyyar APC, Uba Boris, a cikin ƙwaryar Bauchi, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Yan Boko Haram Sun Kai Hari Jihar Yobe da Motocin Yaƙi Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun ritsa abun harin nasu a kan hanyar CBN kusa da gidan mai na AA Rano da misalim ƙarfe 8:00 na daren ranar Laraba.

Yan bindigan, waɗanda suka kai harin a kan mashin guda biyu, sun buɗe wuta domin tsorata mutanen dake wurin, kamar yadda sahara reporters ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel