Sadu da yaron da ya fara koyon yadda ake tuka jirgi a shekara 7
- Wani karamin yaro mai suna Graham Shema ya fara karatun tukin jirgin yana dan shekara 7 bayan mahaifiyarsa ta sanya shi a makarantar koyan tukin jirgin sama
- Shema ya fara sha'awar jiragen sama tun yana dan shekara uku lokacin da helikwafta 'yan sanda ta tarwatsa rufin gidan kakarsa
- Iliminsa ya burge mutane da yawa a kafofin sada zumunta bayan mai amfani da LinkedIn, Elphas Saizi, ya jinjina masa a dandalin
Nahiyar Afirka tana da tarin yan baiwa, kuma wani karamin yaro dan kasar Uganda wanda aka bayyana da suna Graham Shema yana daya daga cikinsu.
A cikin shekarar 2020 lokacin da yake ɗan shekara bakwai a duniya, yaron ya zama abin birgewa a ƙasarsa tare da nuna kwarewarsa a ilimin tukin jirgin sama.
KU KARANTA KUMA: Gwamnan Najeriya ya sauka daga motarsa da daddare, ya shiga sahun masu ba motoci hannu don hana cunkoso
A cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters, Graham wanda yake kaunar lissafi da kimiyya ya tashi a matsayin mai horarwa sau uku a jirgin Cessna 172.
Graham na so ya zama matukin jirgi
Legit.ng ta lura cewa yaron wanda Elon Musk ne gwaninsa ya ce yana son zama matukin jirgi, sannan yayi tafiya har zuwa duniyar Mars wata rana.
A kalamansa:
"Ina son Elon Musk saboda ina so in koyi ilimin sararin samaniya tare da shi, in tafi sararin samaniya tare da shi sannan kuma mu gaisa."
Ta yaya ya fara?
Daily Mail ta ruwaito cewa sha’awar da yaron ke yiwa jirgin sama ya samo asali ne lokacin da helikwaftan ‘yan sanda ya yi kasa sosai sannan ya fasa rufin gidan kakarsa tun yana dan shekara uku.
Bayan wannan lamarin, sai ya fara yiwa mahaifiyarsa tambayoyi kan yadda jirage ke aiki. Dole mahaifiyar ta tuntubi makarantar jirgin sama ta gida kuma ya fara darussa kan sassan jirgin sama da ƙamus ɗin jirgin sama.
Daga baya ya fara daukar darasin tuki. Yayinda yake bayanin tashinsa na farko, Graham yace:
"Na ji kamar tsuntsu yana tashi sama."
Kafofin watsa labarun sun taya Graham murna
Wani mai amfani da LinkedIn mai suna Elphas Saizi ya jinjinawa yaron a shafinsa kuma da yawa sun yi al'ajabi.
Wani bangare na rubutun nasa:
"A cikin kaunar da yake yiwa lissafi da kimiyya, har ma an gayyaci Graham zuwa tarurruka tare da jakadan Jamus da Ministan Sufuri na Uganda."
Da yake martani, Brenda Pooe ya ce:
"Ina jinjinawa mutumin da ya ga kwazonsa. Da yawa sun kasa fahimtar hazakar wasu. Samun damar fahimtar hazakar dan uwanka babbar nasara ce da ba kowa zai iya cimma ba.
"Dubi gwamnatocinmu a Afirka mutane sun kammala karatunsu yayin da suke aiki shekaru da yawa. Yayinda waɗanda suka riga suka sami Digiri na biyu da uku ba su da aikin yi.
"Wannan ƙalubale ne. Gane kwazon ɗan'uwanka ba tare da yin la'akari da yanayin sa ba zai ci babban lokaci ... Huta lafiya .. Na jinjina maka ... dan uwa.”
Birgitta Nortey yayi sharhi:
"Madalla Graham!"
A wani labarin, Kamfanin kera motoci ta Kantanka karkashin jagorancin Shugaban kamfanonin Kantanka Group, ta kera wata sabuwar mota mai suna Kantanka Akofena.
KU KARANTA KUMA: Hotunan mataimakin kwamishinan Ƴan Sanda na bogi da aka kama cikin otel a Kano
A wani wallafa da Legit.ng ta gano a shafin Twitter na shugaban, ya wallafa wani hoto na motar wacce har yanzu ake kan aiki a kanta a kamfanin.
Motar ta Akofena, kamar yadda aka nuno a hoton, tana dauke da suffa iri guda da tsarin motar da Kelvin Odartey, matashi dan shekaru 18 da ke karamar makarantar sakandare ya kera.
Asali: Legit.ng