Badakala: Shugaban EFCC Ya Ci Alwashin Gurfanar da Wani Babba a Jami'iyyar APC

Badakala: Shugaban EFCC Ya Ci Alwashin Gurfanar da Wani Babba a Jami'iyyar APC

  • Shugaban hukumar EFCC ya ci alwashin gurfanar da wani tsohon gwamnan jihar Abia
  • Shugaban ya bayyana cewa, hukumar EFCC za ta ci gaba da tura kararraki zuwa kotu a kasar
  • Hakazalika za ta gurfanar da mutane sama da 800 da ake zargi da laifuka daban-daban a kasar

Shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), Abdulrasheed Bawa, ya sha alwashin cewa hukumar za ta sake gurfanar da tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Kalu.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa Bawa ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da manema labarai a Abuja a ranar Alhamis, 17 ga watan Yuni.

Kalu, wanda yanzu haka dan majalisar dattijai ne, Kotun Koli ta sake shi a kan ka'idoji bayan an same shi da laifin satar biliyoyin nairori lokacin da yake gwamnan jihar Abia tsakanin 1999-2007.

KU KARANTA: An kame wani Fasto da ya kashe matarsa, ya binne gawar a kusa da cocinsa

Badakala: Shugaban EFCC Bawa ya bayyana sunan jigon APC da za a gurfanar
Shugaban Hukumar EFCC, Abdurrasheed Bawa | Hoto: channelstv.com
Asali: Facebook

Ba tare da bayyana asalin karar ba, Kotun Koli ta yanke hukuncin cewa alkalin kotun da ta same shi da laifi an daukaka shi zuwa kotun daukaka kara kuma bai kamata ya yanke hukunci a kan batun ba.

A baya cikin watan Fabrairu an gurfanar Orji Kalu bisa zargin yin sama da fadi kimanin N7.1bn daga kudaden jihar Abia, Vanguard ta ruwaito.

EFCC ta kulla aniyar gurfanar da masu laifin dake hannunta

Bawa ya bayyana cewa EFCC ta kuduri aniyar ci gaba da gabatar da kararraki komai daren dadewa.

Ya bayyana cewa hukumar tana shirin gabatar da sabbin kararraki 800 wadanda suka shafi cin hanci da rashawa da kuma damfarar mutane ta hanyar yanar gizo a kotu.

Shugaban na EFCC ya bayyana cewa yajin aikin da ma'aikatan shari'a suka yi kwanan nan ya jinkirta tura kararrakin daga hukumar.

KU KARANTA: Da Dumi-Dumi: Buhari Ya Isa Borno, Ya Bukaci Sojoji Su Kara Daura Damara

EFCC Ta Bayyana Yadda Ake Sace Kudin Najeriya da Bitcoin, Ta Kwato Miliyoyi

A wani labarin, Shugaban Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arziki Zagon Kasa (EFCC), Abdulrasheed Bawa, ya ce hukumar ta kwato kimanin dala miliyan 20 da barayi a yanar gizo suka wawure.

Mista Bawa, ya bayyana haka ne yayin shirin ‘Sunrise Daily’ na Channels Tv, ya kara da cewa an adana kudaden a cikin asusun yanar gizo na hukumar EFCC, Punch ta ruwaito.

Babban Bankin Najeriya a watan Fabrairun 2021 ya umarci bankuna da sauran cibiyoyin kudi su gano mutane da kungiyoyin da ke musayar kudin Intanet tare da rufe dukkan wadannan asusun.

Hakanan ya bayyana cewa ma'amala da musayar kudade da biyan kudi ta hanyar kudaden intanet haramun ne a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel