Ministan Tsaro Ya Yi Sharhin Kalaman Buhari Na ‘Yaren da Suka Fi Fahimta’

Ministan Tsaro Ya Yi Sharhin Kalaman Buhari Na ‘Yaren da Suka Fi Fahimta’

  • Ministan tsaro a Najeriya ya kare kalaman Buhari na cewa za a bi da 'yan ta'adda da yaren da suke fahimta
  • Ministan ya bayyana cewa, babu laifi don shugaban kasa ya sa an yi kaca-kaca da 'yan ta'adda a Najeriya
  • Hakazalika ya bayyana cewa, duk wani mai aikata laifuka za a hukunta shi, za kuma a bi dashi yadda doka ta tanada

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi daidai da ya ce zai yi maganin masu aikata laifuffukan dake addabar kasar "da yaren da suke fahimta" a cewar ministan tsaron Najeriya, Bashir Magashi.

A cewar ministan tsaron, babu wani aibi don shugaban kasar ya kawar da masu shirin hargitsa kasar, in ji The Cable.

Magashi ya ce:

“Ba yadda za a yi ku mallaki makami ba bisa ka’ida ba kuma a bar ku ku rayu saboda ana iya amfani da makamin a kanku.

KARANTA WANNAN: Jerin Ministocin Buhari da Basu da Kwalin NYSC da Kuma Dalilan da Suka Jawo

Ministan Tsaro ya kare kalaman Buhari na 'Magana ga 'yan ta'adda da yaren da suke fahimta'
Ministan tsaro na Najeriya | Hoto: kanyidaily.com
Asali: UGC

“Za mu dauki mataki kan duk wanda yake dauke da makamai. Najeriya ba za ta bari hakan ya ci gaba da faruwa ba. Wannan shine sakonmu. ”

Da yake ci gaba da bayani, ya sha alwashin cewa za a hukunta masu aikata laifuka a kasar nan domin doka za ta bi dasu yadda ya dace.

Ya kara da cewa:

“Idan ka aikata laifi, za a kama ka, a gurfanar da kai kuma idan an kama ka da laifi za a hukunta ka. Amma ga duk wanda ya yi amfani da makami a kan soja, kun san abinda hakan ke nufi kuma za mu bi dashi yadda doka ta tanada."

Hakan jahilci ne: Minista Malami ya caccaki lauyan turai da ya kare Nnamdi Kanu

Kelechi Amadi ya hadu da fushin Ministan Sharia game da kalamansa kan kama Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar IPOB.

Ministan na kasar Kanada ya sha caccaka daga babban lauyan tarayya kuma ministan shari’a, Abubakar Malami inda ya yi masa wankin babban bargo, inji rahoton The Cable.

A kwanakin baya ne Madu ya caccaki Minista Malami game da kamun Nnamdi, yana mai cewa idan har da gaske an kama Kanu ba bisa ka'ida ba aka dawo da shi Najeriya, to Malami ya zama abun kunya ga doka da oda.

KARANTA WANNAN: Gamayyar Arewa Ta Zargi Gwamnonin Kudu da Ba Nnamdi Kanu da Sunday Igboho Mafaka

Shugaba Buhari ya jinjina wa jami'an tsaro bisa kame Nnamdi Kanu da farautar Igboho

A wani labarin, Fadar shugaban kasa ta jinjinawa hukumomin tsaron Najeriya game da kamun Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar IPOB, da harin da aka kai kwanan nan a gidan Sunday Igboho, dan rajin kare hakkin Yarbawa da ke Ibadan.

A cikin wata sanarwa da ta fito ta hannun mai taimaka wa shugaban kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, fadar shugaban kasar ta kuma yaba wa hukumomin kasashen duniya wadanda suka ba da hadin gwiwarsu ga hukumar bincike ta kasa (NIA) har aka kamo Kanu.

Rahoton ya kara da cewa IPOB, karkashin jagorancin dan yankin kudu maso gabas da ya ke fafutukar ballewa, ta zama kungiyar da ta yi kaurin suna wajen aikata kisan kai da maganganun batanci wadanda za su iya ruruta wutar fitina a Najeriya, jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.