Cikakken Bayani: Yan Boko Haram Sun Kai Hari Jihar Yobe da Motocin Yaƙi

Cikakken Bayani: Yan Boko Haram Sun Kai Hari Jihar Yobe da Motocin Yaƙi

  • Yan Boko Haram sun kai hari yanki a jihar Yobe da safiyar Alhamis a cikin motar sulƙe
  • Maharan sun mamaye ƙauyen da misalin ƙarfe 10:00 na safe, yayin da mutanen garin suka arce
  • Wasu mazauna ƙauyen sunce da yuwuwar yan ta'addan sun zo ɗibar kayan abinci ne

Wasu da ake zargin yan ta'addan Boko Haram ne sun kai hari ƙauyen Katarko mai nisan kilomita 18 tsakaninsa da Damaturu, babban birnin jihar Yobe, kamar yadda channels tv ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Da Ɗuminsa: Yan Bindiga Sun Sake Yin Awon Gaba da Aƙalla Mutum 13 a Kaduna

Mazauna garin sun shaida wa manema labarai a ranar Alhamis cewa maharan sun shiga ƙauyen da misalin ƙarfe 10:00 na safe a cikin motar sulke ta yaƙi da kuma motoci Hilux guda 6 ɗauke da bindigun kakkaɓo jirgi,.kamar yadda sahara reporters ta ruwaito.

Boko Haram ta kai hari Yobe
Yanzu-Yanzu: Yan Boko Haram Sun Kai Hari Jihar Yobe da Motocin Yaƙi Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Wasu mazauna ƙauyen da suka tsere cikin daji domin tseratar da rayuwarsu, sun bayyana cewa suna tsammanin yan ta'addan sun zo satar kayan abinci ne saboda yau Alhamisa ranar Ƙasuwar ƙauyen Katarko ce.

"Muna ganin sun zo ɗibar kayan abinci ne saboda ranar Alhamis itace ranar da kasuwa take ci a ƙauyen Katarko," inji su.

Sojoji sun musu kwantan ɓauna

Wata majiya ta bayyana cewa jami'an soji sun yi wa yan ta'addan kwantan ɓauna yayin da suke ƙoƙarin komawa sansanin su.

KARANTA ANAN: Ma'aikata 774,000: FG Ta Bayyana Abinda Take Shiryawa Ma'aikatan SPW Bayan Gama Biyansu N60,000

Harin ƙarshe da aka kai Ƙauyen Katarko shine wanda aka kai ranar 16 ga watan Maris, inda yan ta'addan suka lalata gine-gine wurin kula da lafiƴar mutane.

A wani labarin kuma Yan Bindigan da Suka Sace Ɗalibai a Kaduna Sun Yi Watsi da Buhun Shinkafa 9 da Aka Kai Musu

Hukumar makarantar Bethel Baptist ta ce ta kaiwa yan bindiga buhun shinkafa 9 amma sun ƙi amsa.

Yan bindigan da suka sace ɗaliban makarantar a Kaduna sun nemi iyaye da hukumar makarantar su bada abinci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel