Karin Bayani: Yan Bindiga Sun Sake Yin Awon Gaba da Aƙalla Mutum 13 a Kaduna
- Wasu yan bindiga sun yi awon gaba da aƙalla mutum 13 a ƙauyen Unguwan Gimbiya dake yankin sabo
- Wannan na zuwa ne kwana biyu bayan sace ɗalibai sama da 120 a wata sakandire dake Maraban Rido
- Fusatattun matasan yankin sun fito kan hanyar Sabon Tasha-Kachia suna zanga-zanga kan harin
Aƙalla mutum 13 wasu yan bindiga suka yi awon gaba da su a ƙauyen Unguwan Gimbiya dake yankin Sabo, ƙaramar hukumar Chukun, jihar Kaduna, kamar yadda thisday ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Ma'aikata 774,000: FG Ta Bayyana Abinda Take Shiryawa Ma'aikatan SPW Bayan Gama Biyansu N60,000
Rahoton Leadership ya nuna cewa lamarin ya faru ne a ranar Laraba da misalin ƙarfe 11:00 na dare.
Daga cikin waɗanda aka sace harda wani mai bada hayar gidaje da kuma masu haya, waɗanda aka yi awon gaba da su a gida ɗaya.
Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa maharan sun mamaye ƙauyen da misalin ƙarfe 11:00 na daren Laraba ɗauke da manyan makamai, inda suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi.
Yace: "Ba wanda zai iya wani ƙoƙari saboda maharan na ɗauke da muggan makamai kuma sun zo da yawa."
"A halin yanzun bamu san adadin mutanen da suka ɗauke ba, amma dai sun tafi da mutane da yawa."
Wannan na zuwa ne awanni 48 bayan wasu yan bindiga sun yi awon gaba da ɗalibai sama da 120 daga makarantar Bethel Baptist dake Maraban Rido.
Mutun 14 aka sace a harin
Tsohon shugaban ƙaramar hukumar Chukun, Sama'ila Leeman, ya bayyana cewa maharan sun yi awon gaba mutum 14.
Yace: "Maharan na isa ƙauyen suka buɗe wuta domin su tsorata mutanen garin, kafin daga bisa ni su shiga wasu gidaje, inda suka sace mutum 14."
KARANTA ANAN: Rikicin Siyasa: Jam'iyyar APC Ta Gayyaci Ministan Buhari Kan Wani Zargi
Matasa sun fita zanga-zanga
A halin yanzun, adadi mai yawa na fusatattun matasa sun fito kan hanyar Sabon Tasha-Kachia suna zanga-zanga da safiyar Alhamis kan yawaitar kai hari yankinsu.
Masu zanga-zangar sun toshe hanyar baki ɗaya, wanda hakan ya janyo tara abubuwan hawa a hanyar.
Kakakin yan sanda na jihar Kaduna, Muhammad Jalige, yaƙi tabbatar da lamarin kai tsaye, amma ya bayyana cewa zai sanar a hukumance da zaran ya samu cikakken rahoto.
A wani labarin kuma Wasu Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Shugaban Fulani, Jamhuro Sule
Wasu yan bindiga sun yi awon gaba da shugaban fulani, Alhaji Usmanu Sule, yayin da yakai ziyara ƙauye.
Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun kutsa har cikin gida kuma suka tafi da shi.
Asali: Legit.ng