Rikicin Siyasa: Jam'iyyar APC Ta Gayyaci Ministan Buhari Kan Wani Zargi

Rikicin Siyasa: Jam'iyyar APC Ta Gayyaci Ministan Buhari Kan Wani Zargi

  • Jam'iyyar APC ta ƙasa ta aike da takardar gayyata ga ministan yaɗa labarai da al'adu, Alhaji Lai Muhammed
  • APC ta gayyaci ministan ne ya zo ya mata bayani kan dalilin buɗe wata sabuwar sakateriya a jihar Kwara
  • Cece-kuce ya ɓarke tsakanin ministan yaɗa labarai da gwamnan Kwara, AbdulRahman

Kwamitin riƙo na jam'iyyar APC ta ƙasa ya gayyaci ministan yaɗa labarai da al'adu, Alhaji Lai Muhammed a kan wata sakateriya da ya buɗe a Ilorin, jihar Kwara, kamar yadda the nation ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Da Dumi-Ɗumi Wasu Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Shugaban Fulani, Jamhuro Sule

Sakateriyar jam'iyyar ta ƙasa ta aike wa ministan da takardar gayyata domin yazo ya mata bayani kan dalilin da yasa yayi haka da kuma matakin ladaftarwa a kansa, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Hedkwatar APC ta jihar Kwara tana yankin Tanke yayin da ministan ya buɗe wata hedkwatar a ɓangarensa a GRA Ilorin.

APC ta gayyaci Lai Muhammed
Rikicin Siyasa: Jam'iyyar APC Ta Gayyaci Ministan Buhari Kan Wani Zargi Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Shugaban APC ta Kwara yace za'a ɗauki mataki

Shugaban kwamitin riƙo na APC a Kwara, Abdullahi Samari Abubakar, ya bayyana cewa ministan zai fuskanci hukunci kan zargin yiwa jam'iyya zagon ƙasa.

Abubakar ya shaida wa manema labarai cewa APC zata yi abinda ya dace kamar yadda kundin tsarin jam'iyyar ya tanazar.

KARANTA ANAN: Ma'aikata 774,000: FG Ta Bayyana Abinda Take Shiryawa Ma'aikatan SPW Bayan Gama Biyansu N60,000

Ba zance komai ba game da gayyatar minista Lai

Sakataren APC na ƙasa, John James Akpanudoedehe, yace ba zai iya tabbatar da gayyatar ba kuma ba zai ƙaryata ba, amma APC ba zata kyale duk wanda yayi ƙoƙarin raba APC a kowane mataki ba.

Akpanudoehede, ya ƙara da cewa kwamitin riƙo ya duƙufa domin tabbatar da zaman lafiya a cikin jam'iyya kuma a kowane mataki sabida haka "akwai buƙatar a gayyaci ministan ya amsa tambayoyi."

"Minista babban mutum ne kuma wajibi ne mu girmama shi, ba zamu so wani abu mara daɗi ya same shi ba. Amma a ɓangare ɗaya, APC ba zata kyale ko waye ya saɓawa dokokinta ba." inji shi.

A wani labarin kuma Dokar Hana Makiyaya Kiwo a Fili Ba Zata Yi Aiki Ba, Inji Gwamna Zulum, Ya Faɗi Dalili

Gwamna Zulum na jihar Borno , yace dokar hana fulani makiyaya kiwo a fili ba za ta yi aiki ba.

Gwamnan yace abinda ya kamata a maida hankali akai shine lalubo hanyar magance matsalar tsaro da ta abinci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel