Matar mutum kabarinsa: Matashi ya angwance da wata budurwa duk da nakasar da take da ita

Matar mutum kabarinsa: Matashi ya angwance da wata budurwa duk da nakasar da take da ita

  • Wani matashi daga garin Bauchi ya taba zukatan jama’a da dama bayan ya yi wani bajinta da ba kowa ne zai iya ba
  • Matashin ya auri wata budurwa wacce ta samu nakasa sakamakon konewa da fuskarta da wuyarta suka yi
  • Yanayin nakasar matar ya sanya mutane suna kyamarta tare da nuna mata tsangwama

Mabiya shafukan sada zumunta sun tofa albarkacin bakunansu bayan bayyanar hotunan wasu ma’aurata. Angon wanda ya fito daga garin Bauchi ya taba zukatan mutane da dama tare da burgesu sakamakon jihadin da yayi.

Matashin dai ya auri wata matashiya ce dake fama da nasaka ta kuna a wuyarta da fuskarta.

KU KARANTA KUMA: AfDB ta nada Barrow a matsayin sabon shugaban ofishinta na Najeriya

Matar mutum kabarinsa: Matashi ya angwance da wata budurwa duk da nakasar da take da ita
Matashin ya auri matar tasa duk da nakasar da take da ita Hoto: gulmanzamani
Asali: Instagram

Wani shafin Instagram mai suna gulmanzamani ya wallafa cewa jama’a na nuna kyama da tsangwama ga matashiyar saboda yanayin lalurarta, harta kai yara kan ji tsoro idan suka kalle ta.

Wannan hali da yarinyar ke ciki ya sanya saurayin ya nemi yardar iyayensa inda a yanzu suka zamo mata da miji.

Shafin ya wallafa:

“Daga garin bauchi, wannan yaro da kuke gani yayi abin da ya taba zukatar dumbun mutane, ganin yanayi da halin da yarinyar nan take ciki na nakasar da ta sameta na quna a fuskarta da wuyarta, wanda ya jawo ma kyama da tsangwama da kuma tsoronta da yara sukeyi, hakane yasa ya aureta da yardan iyayensa, yanzu haka cikin ikon Allah yanzu haka sun zamo miji da mata, yadda ya rufa mata asiri shima allah ya masa duniya da lahira. Ameen ya rabb.”

Jama’a sun yi martani a kan sadaukarwar matashin

Wannan abu ya burge mabiya shafukan sadarwa inda suka tofa albarkacin bakunansu tare da sanyawa ma’auratan albarka.

KU KARANTA KUMA: Ana Kokarin Soke NYSC, Amma Gwamna Ya Nemi a Mayar da Shirin NYSC Shekara Biyu

nafisagwarzo ta yi martani:

“Amin Ya Rabbal Alamina lallai yayi jahadi. Allah ya saka masa da mafificin alkhairinsa.”

fatiezee ta ce:

“Wannan abinda yayi ma ya soma jawo masu alkhairi. Na san za ma ta samu ayi mata aiki.”

skinhaven68 ya rubuta

“Allah ya albarkaci aurensu.”

_bambiee ya yi martani:

“Tabbas na yarda duk yanda kake akwai mai sanka Wallahi Allah ya basu zaman lafiya ya saka Mashi da alkairi .”

syraj_ ya ce:

“Dan Allah ina nemanshi na mashi babban kyauta.”

mrsadeeque ta rubuta:

“Allah ya basu Zaman lfy kuma Allah yasa sanadiya arzikinshice duniya da lahira ya Kuma bata ikon yi masa biyayya.”

Bayan kin amincewa da aurensa, matashi ya sayawa budurwa tsaleliyar mota

A wani labari na daban, wani matashi mai suna @Turkcooper a TikTok ya baiwa budurwarsa da yaso ya aura sabuwar mota duk da cewa ta ce ba zata auresa ba.

Yayin bada labarin abinda yayi a faifan bidiyo da ya daura a shafinsa, matashin ya rufewa yarinyar ido domin bata mamaki da babbar motar.

Duk da cewa ta ce ba zata auresa, budurwar ta karbi sabuwar motar da hannu biyu kuma ta dane ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel