Bayan kin amincewa da aurensa, matashi ya sayawa budurwa tsaleliyar mota

Bayan kin amincewa da aurensa, matashi ya sayawa budurwa tsaleliyar mota

  • Wani babban yaro ya bayyana yadda ya sayawa budurwa sabuwar mota bayan ta ki amincewa da aurensa
  • Matashin ya baiwa budurwar mamaki kan wannan gagarumin kyauta da yayi mata
  • Duk da cewa tace ba zata auresa ba, ta karbi kyautar motar

Wani matashi mai suna @Turkcooper a TikTok ya baiwa budurwarsa da yaso ya aura sabuwar mota duk da cewa ta ce ba zata auresa ba.

Yayin bada labarin abinda yayi a faifan bidiyo da ya daura a shafinsa, matashin ya rufewa yarinyar ido domin bata mamaki da babbar motar.

Budurwar ta karbi motar

Duk da cewa ta ce ba zata auresa, budurwar ta karbi sabuwar motar da hannu biyu kuma ta dane ciki.

DUBA NAN: Ba zan bari ’yan bindiga su samu gindin zama a Bauchi ba - Bala Mohammed

Kalli bidiyon:

Da kamar wuya dai a samu matashin da zai yi irin wannan abu ga yarinyar da ta wasa masa kasa a ido.

Matashi ya sayawa budurwa tsaleliyar mota
Bayan kin amincewa da aurensa, matashi ya sayawa budurwa tsaleliyar mota Hoto: @factsandtruths_official
Asali: UGC

KU KARANTA: Za'a fita duba watan Zhul-Hajji ranar Juma'a a kasar Saudiyya

Daga bashi kudin tallafi, ya kara aure

Wata Kungiya mai zaman kanta (NGO) ta bayar da gudummawar N100,000 ga wani magidancin da ke fama da yadda zai dauki nauyin iyalinsa da zimmar ya kama harkar kasuwanci.

Sai dai abin mamaki a nan, magidancin ya buge da kashe dukkan kudaden wajen kara aure, kamar yadda wata mai amfani da kafar sada zumunta da sunan @purpleandflawed ta wallafa a shafinta na sada zumuntar,

Ta ce mutumin ya yanke shawarar kashe kudin ne wajen shirya bikin auren mata ta biyu, a maimakon yayi amfani da tallafin kan sharadin da aka ba shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel