Da Ɗumi-Ɗumi: Yan Bindigan da Suka Sace Ɗalibai a Kaduna Sun Kira Makarantar Ta Wayar Salula

Da Ɗumi-Ɗumi: Yan Bindigan da Suka Sace Ɗalibai a Kaduna Sun Kira Makarantar Ta Wayar Salula

  • Yan bindigan da suka kai hari makarantar Bethel Baptist a jihar Kaduna sun kira makarantar ta waya
  • Shugaban makarantar ya bayyana cewa an samu damar yin magana da wasu daga cikin ɗaliban
  • Ɓarayin sun tabbatar da cewa ɗaliban dake hannun su 121 ne kuma suna cikin ƙoshin lafiya

Yan bindigan da suka sace ɗalibai a makarantar sakandiren Bethel Baptist, jihar Kaduna sun tabbatar da cewa sun sace ɗalibai 121, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamna Ya Ɗage Dokar Hana Fita da Ya Sanya a Jiharsa Tsawon Wata 2

Shugabam makarantar Bethel Baptist dake Kaduna, Rev. Yahaya Adamu Jangado, shine ya bayyana haka ga manema labarai ranar Talata.

Ya ƙara da cewa ɓarayin sun sanarwa hukumar makaranta cewa ɗaliban da suka sace suna nan cikin ƙoshin lafiya, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Yan bindiga sun kira waya
Da Ɗumi-Ɗumi: Yan Bindigan da Suka Sace Ɗalibai a Kaduna Sun Kira Makarantar Ta Wayar Salula Hoto: dailytrust.com
Source: UGC

A cewarsa, Makaranta ta samu damar magana da wasu daga cikin ɗaliban, wanda sune suka tabbatar da yawansu kamar yadda maharan suka sanar musu.

Yace: "A yau Talata mun samu kira daga yan bindiga kuma sun tabbatar mana da cewa 'yayan mu suna cikin ƙoshin lafiya."

"Mun samu damar magana da wasu daga cikin ɗaliban, sun ƙirga kansu a wurin da suke tsare kuma suka faɗa mana mutun 121 ne."

"Kuma da muka haɗa adadin su da kuma waɗanda suka dawo, sai muka samu yawan ɗaliban da muke da su a ɗakin kwanan."

KARANTA ANAN: Yan Bindiga Sun Kutsa Kai Wata Sananniyar Kasuwa, Sun Yi Awon Gaba da Kayan Masarufi da Dama

Hukumar makaranta ta kira iyayen ɗalibai

Mr. Jangado ya ƙara da cewa hukumar makaranta ta kira iyayen yaran ta kuma yaba musu da halin dattakon da suka nuna wajen fahimta, hakuri, juriya da kuma ƙoƙarin taimakawa duk da irin halin da suke ciki.

Yace an sanar da gwamnati, kuma ta yi alƙawarin yin duk me yuwuwa domin ganin ɗaliban sun dawo cikin ƙoshin lafiya.

A wani labarin kuma El-Rufa'i Ya Kafa Hukumar da Zata Binciki Yajin Aikin NLC da Ayuba Waba ya Jagoranta a Kaduna

Gwamnatin Kaduna ta kafa hukumar da zata bincike yajin aikin da ƙungiyar ƙwadugo ta gudanar a jihar a watan Mayu

Kakakin gwamnan jihar, Mr. Muyiwa Adekeye, shine ya bayyana haka a wani jawabi da ya fitar ɗauke da sa hannunsa

Source: Legit.ng

Online view pixel