Batun Daukaka Magu: PDP ta zargi shugaba Buhari da goyon bayan cin hanci da rashawa

Batun Daukaka Magu: PDP ta zargi shugaba Buhari da goyon bayan cin hanci da rashawa

  • Jam'iyyar PDP ta yi kaca-kaca da batun da ke cewa za a kara wa Magu girma zuwa wani matsayi
  • PDP ta nuna damuwarta da cewa, ya kamata a ci gaba da bincikar Magu sannan a gurfanar dashi
  • Hakazalika jam'iyyar ta shawarci shugaba Buhari kan cewa, kada ya sassauta wajen yaki da cin hanci

Jam’iyyar PDP ta yi tir da kakkausar murya game da shirin da fadar shugaban kasa ta yi na daukaka tsohon shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), Ibrahim Magu zuwa rundunar ‘yan sandan Najeriya (NPF).

Rahotannin da ba a tabbatar da su ba sun yadu a kafafen watsa labarai na yanar gizo cewa za a tura Magu zuwa ofishin Mataimakin Sufeto-Janar (AIG) ta Hukumar Kula da 'Yan sanda (PSC), The Cable ta rahoto.

Da take bayyana matakin da ake yadawa a matsayin wuce gona da iri, PDP a wata sanarwa a ranar Talata, 6 ga watan Yuli, ta ce hakan cin fuska ne ga idon 'yan Najeriya.

KARANTA WANNAN: Ghali Na'Abba Ya Yi Martani Kan Kame Nnamdi Kanu da Farautar Sunday Igboho

Batun Daukaka Magu: PDP ta zargi shugaba Buhari da goyon bayan cin hanci da rashawa
Tsohon Shugaban EFCC, Ibrahim Magu | Hoto: dailytrust.com.ng
Asali: Twitter

Jam’iyyar adawar ta nuna cewa ta wannan shirin na daukaka Magu wanda ke fuskantar tuhume-tuhume da dama da suka hada da halatta kudin haram, daidai yake da ace gwamnatin tarayya na inganta cin hanci da rashawa a bayyane.

A cikin bayanin Kola Ologbondiyan, kakakin jam'iyyar, PDP ta tuno cewa Babban Lauyan Tarayya (AGF) Abubakar Malami da kuma hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) tuni sun gabatar da rahoto kan Magu wanda kwamitin shari’a Ayo Salami ya jagoranta ya amince da shi.

Saboda da haka PDP ta shawarci hukumar 'yan sanda da ta yi tirkiya kan yunkurin daukaka Magu zuwa hukumar.

Ta ci gaba da cewa:

"PDP na kara ba Shugaba Buhari shawara da kada ya "sassauta" zargin cin hancin da ake yi kan Magu sai dai ma kamata yayi a bude rahoton Justice Salami idan ya cancanta, a gurfanar da tsohon shugaban na EFCC."

Za a yi wa Magu karin girma zuwa AIG duk da zargin rashawa

Hukumar kula da al'amuran 'yan sanda ta shirya tsaf domin yi wa Ibrahim Magu, tsohon mukaddashin shugaban hukumar yaki da rashawa da hana yi wa kasa zagon kasa (EFCC), karin girma zuwa mataimakin sifeta janar na 'yan sanda a wannan makon, TheCable ta fahimci hakan.

Magu, wanda aka karawa girma zuwa kwamishinan 'yan sanda a 2018, an bukaci cireshi daga matsayin shugaban EFCC bayan kammala binciken kwamitin Jastis Ayo Salami bayan an zargesa da yin amfani da kujerarsa ba yadda ya dace ba.

Kwamitin ya bukaci a tsige Magu daga kujerarsa saboda kasa bayyana inda kudade har N431,000,000 na kudin yada labarai da aka sakarwa ofishin shugaban hukumar EFCC tsakanin watan Nuwamba na 2015 zuwa Mayun 2020 suke.

KARANTA WANNAN: Karin Bayani: Gwamnonin Kudu sun ce basu amince a sake kame wani a yankinsu ba sai da izininsu

An zargesa da bata da duk wata shaida tare da hanawa tare da dakile duk wasu hanyoyin bincike a wani bincike da ake yi da ya hada da tsohon shugaban majalisar tarayya da tsohon manajan darakta PPMC.

Magu: Yadda ake kwashe 'ruwan' N550bn da EFCC ta kwato

A wani labarin daban, Kwamitin fadar shugaban kasa na bayani a kan kadarorin da aka dawo da su a Hukumar yaki da rashawa karkashin dakataccen mukaddashin shugaban hukumar, Ibrahim Magu.

Kwamitin na binciken kadarorin gwamnati da EFCC ta kwato daga Mayun 2015 zuwa Mayun 2020.

Kwamitin ya sanar da cewa an kwashe rarar da aka samu a kan kudi har N550 biliyan da aka samu a karkashin shugabancin Magu, kamfanin dillancin labaran Najeriya ya ruwaito. Kwamitin ya ce an kasa bada bayani a kan rarar samar kudin da aka samu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel