El-Rufa'i Ya Kafa Hukumar da Zata Binciki Yajin Aikin NLC da Ayuba Waba ya Jagoranta a Kaduna

El-Rufa'i Ya Kafa Hukumar da Zata Binciki Yajin Aikin NLC da Ayuba Waba ya Jagoranta a Kaduna

  • Gwamnatin Kaduna ta kafa hukumar da zata bincike yajin aikin da ƙungiyar ƙwadugo ta gudanar a jihar a watan Mayu
  • Kakakin gwamnan jihar, Mr. Muyiwa Adekeye, shine ya bayyana haka a wani jawabi da ya fitar ɗauke da sa hannunsa
  • A cewar jawabin hukumar na cikin kundin tsarin mulki na 1999, kuma akwai ayyuka da dama da aka ɗora mata

Gwamnatin Kaduna ta kafa hukumar da zata binciki yajin aikin da ƙungiyar NLC ta gudanar a jihar a watan Mayu 2021, wanda mai ritaya Alkali Ishaq Bello, zai jagoranta, kamar yadda channels tv ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Yanzu-Yanzu: Yan Sanda Sun Kuɓutar da Mai Baiwa Gwamna Shawara da Aka Sace Cikin Awanni 5

Wannan na ƙunshe ne a wani jawabi da kakakin gwamna Malam El-Rufa'i, Muyiwa Adekeye, ya fitar ɗauke da sanya hannunsa.

Ya bayyana cewa tsohon Antoni Janar na jihar Cross River, Eyo Ekpo, da kuma tsohon antoni janar na Kaduna, Joan Jatau Kadiya, na daga cikin mambobin hukumar, kamar yadda daily Nigerian ta ruwaito.

Gwamna El-Rufa'i
El-Rufa'i Ya Kafa Hukumar da Zata Binciki Yajin Aikin NLC da Ayuba Waba ya Jagoranta a Kaduna Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Hakanan tsohon mataimakin sakataren ƙungiyar NLC kuma mataimakin sakataren ƙungiyar yan jarida, NUJ, Chom Bagu, yana daga cikin mambobi.

Sauran mambobin sun haɗa da, AVM Rabiu Dabo, Nasirudeen Usman, da kuma Mohammed Isah Aliyu.

KARANATA ANAN: Kungiyar Ƙwadugo NLC Ta Janye Yajin Aikin da Ta Kwashe Mako 3 Tana Yi

Ayyukan dake kan sabuwar hukumar

A cewar jawabin: "Hukumar binciken tana cikin kundin tsarin mulki na 1999, da kuma dokar hukumar bincike CAP 34, dokokin jihar Kaduna 1991."

"Binciken ya ƙunshi abubuwa 14 da suka haɗa da, bincike kan haramcin yajin aikin gargaɗi, da ayyukan da wasu ɗai-ɗaikun mutane suka yi da ƙungiyoyi."

"Zata bincike adadin kuɗaɗen shiga da aka rasa a lokacin wannan yajin aiki, sannan kuma ta bada shawarwarin matakin da za'a ɗauka, wanda ya haɗa da gurfanarwa a gaban kotu da sauransu."

A wani labarin kuma Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 2, Sun Yi Awon Gaba da Shanu da Dama a Jihar Katsina

Yan bindiga sun sake kai hari jihar Katsina, inda suka hallaka mutum 2, sannan suka yi awon gaba da shanu.

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun mamaye ƙauyukan Ajiya da Yasore da sanyin safiyar Lahadi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel