Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamna Ya Ɗage Dokar Hana Fita da Ya Sanya a Jiharsa Tsawon Wata 2
- Gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers, ya ɗage dokar hana fita da daddare da gwamnatinsa ta sanya
- Gwamnatin jihar Rivers ta sanya dokar hana fita da daddare saboda yawaitar kaiwa jami'an tsaro hari
- Gwamnan ya roƙi mazauna jihar da su yi gaggawar kai rahoton duk wani abu da basu amince da shi ba
Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ya ɗage dokar hana fita da ya sanya a jihar watanni biyu da suka gabata saboda yawaitar hare-haren yan bindiga, kamar yadda punch ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Yan Bindiga Sun Kutsa Kai Wata Sananniyar Kasuwa, Sun Yi Awon Gaba da Kayan Masarufi da Dama
Gwamnan yace ɗage dokar zai fara aiki ne daga ranar Laraba 7 ga watan Yuli, 2021.
Gwamna Wike, wanda ya bayyana haka a wani shiri da aka watsa kai tsaye ranar Talata, yace gwamnati ta gano illar dokar a kasuwanci da kuma walwala a jihar da mazaunan jihar.
Mai taimakawa gwamna Wike ta ɓangaren watsa labarai, Kelvin Ebiri, ya haɗa bayanan gwamnan a wani jawabi da ya yi wa take da "Gwamna Wike ya ɗage dokar hana fita da daddare a Rivers" kuma a ka raba wa manema labarai a Patakwal.
Gwamnan yace an ɗauki wannan matakin ne saboda cigaban da aka samu a ɓangaren tsaron jihar da na maƙotanta.
Yace: "Gwamnati ta yanke hukuncin ɗage dokar hana fita daga gobe Laraba 7 ga watan Yuli, 2021."
KARANTA ANAN: El-Rufa'i Ya Kafa Hukumar da Zata Binciki Yajin Aikin NLC da Ayuba Waba ya Jagoranta a Kaduna
Gwamnan ya yaba da biyayyar al'ummar jihar Rivers
Yayin da yake godiya ga al'ummar jihar bisa fahimtar su da haɗin kan da suka bayar lokacin da aka sanya dokar, Wike ya roƙi mutane da su kasance a ankare dangane da tsaro kuma su gaggauta kai rahoton abinda ba su yarda da shi ba ga jami'an tsaro.
"A ɓangaren gwamnati, ba zamu gajiya ba wajen tura duk abinda muke da shi don tabbatar da tsaron lafiyar mutane da dukiyoyinsu." inji Wike.
A wani labarin kuma Yan Sanda Sun Kuɓutar da Mai Baiwa Gwamna Shawara da Aka Sace Cikin Awanni 5
Rundunar yan sanda ta samu nasarar kuɓutar da mai baiwa gwamna Ayade hsawara da aka sace, kamar yadda daily trust ta ruwaito.
Wasu yan bindiga aƙalla goma sun sace mai baiwa gwamna Cross Rivers shawara kan noman Cocoa.
Asali: Legit.ng