Yan Bindiga Sun Kutsa Kai Wata Sananniyar Kasuwa, Sun Yi Awon Gaba da Kayan Masarufi da Dama

Yan Bindiga Sun Kutsa Kai Wata Sananniyar Kasuwa, Sun Yi Awon Gaba da Kayan Masarufi da Dama

  • Yan bindiga sun kusta cikin wata sananniyar kasuwar supermarket a jihar Enugu
  • Rahotanni sun bayyana cewa yan bindigan ba su cutar da kowa ba amma sun yi awon gaba da kayan masarufi
  • Wani ma'aikaci a kasuwar ya bayyana cewa da farko ya ɗauka jami'an gwamnati ne suka zo bincike

Yan bindiga sun kai hari wani sananne kuma baban kanti 'supermarket' mai suna "Uzorbest Super-market Limited," dake Onu Asata, jihar Enugu, kamar yadda Punch ta ruwaito.

KARANTA ANAN: El-Rufa'i Ya Kafa Hukumar da Zata Binciki Yajin Aikin NLC da Ayuba Waba ya Jagoranta a Kaduna

Rahotanni sun bayyana cewa ɓarayin sun yi awon gaba da buhunan shinkafa yar ƙasar waje 18, shinkafa ta cikin gida 10, katan ɗin taliya 50 da kuma buhunan semolina 20.

Yan bindigan sun kuma yi awon gaba da gas ɗin girki guda 4 daga wani shago dake kusa da kasuwar supermarket ɗin, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Yan bindiga sun kai hari kasuwar supermarket
Yan Bindiga Sun Kutsa Kai Wata Sananniyar Kasuwa, Sun Yi Awon Gaba da Kayan Masarufi da Dama Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Hukumar dillancin labarai NAN, ta gano cewa maharan sun kai hari kasuwar ne a cikin motar Hilux da misalin ƙarfe 6:00 na yammacin ranar Litinin.

Ɗaya daga cikin ma'aikatan wurin, Mr Sunday Ngwoke, ya shaidawa manema labarai cewa maharan sun kai aƙalla 15, duka sun rufe fuskansu da baƙin ƙyalle, sannan ɗaya daga cikinsu ya dinga magana da ƙarfi yana cewa "ku ɗakko wannan buhun"

Yace: "Da farko na ɗauka jami'an gwamnati ne suka zo duba ingancin kayayyakin mu, shiyasa nayi ƙoƙarin zuwa wurin ɗaya daga cikinsu in hana shi ɗaukar wani buhu, amma ina ganin katuwar bindiga sai na tsorata na ja da baya."

"Sun ɗauki gaba ɗaya abubuwan da na faɗa muku da farko sun ɗora a motarsu, kafin subar wurin sai da suka buɗe wuta a sama, suka tsorata kowa dake wurin ."

"Mun gode wa Allah babu wanda suka cutar kuma basu ɗauki ko sisi ba, sai kayan abinci."

KARANTA ANAN: Yanzu-Yanzu: Yan Sanda Sun Kuɓutar da Mai Baiwa Gwamna Shawara da Aka Sace Cikin Awanni 5

Yan sanda basu san da lamarin ba

Kakakin rundunar yan sandan Enugu, Daniel Ndukwe, ya bayyana cewa hukumar yan sanda bata samu wani rahoto kan lamarin daga DPO dake yankin ba.

"Zamu tuntuɓi DPO na yankin domin jin abinda ya faru, ina tabbatar muku hukumar yan sanda zata fitar da jawabi kan lamarin da zaran ta gano ainihin abinda ya faru." inji shi.

A wani labarin kuma Kungiyar Ƙwadugo NLC Ta Janye Yajin Aikin da Ta Kwashe Mako 3 Tana Yi

Ƙungiyar ƙwadugo a jihar Nasarawa ta sanar da janye yajin aikin da ta shafe makonni uku tana gudanarwa.

Ƙungiyar ta amince da wannan matakin ne bayan cimma wata yarjejeniyar fahimta da ɓangaren gwamnatin jihar.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel