Hotuna sun bayyana yayin da gwamnonin arewa maso gabas suka isa Taraba don ganawa mai muhimmanci

Hotuna sun bayyana yayin da gwamnonin arewa maso gabas suka isa Taraba don ganawa mai muhimmanci

  • Gwamnonin Najeriya daga yankin arewa maso gabas na jam’yyun PDP da APC sun hallara a jihar Taraba
  • Ana sa ran Gwamna Darius Ishaku ne zai tarbi Shugabannin jihohin da ke karkashin kungiyar gwamnonin arewa maso gabas (NEGF)
  • Gwamnonin na jihohi shida da za su gana a karon farko za su tattauna batutuwan da suka shafi ci gaban yankin

Gwamna Darius Dickson Ishaku na Taraba zai karbi bakuncin takwarorinsa na shiyyar arewa maso gabas a Jalingo, babban birnin jihar.

Bala Dan Abu, babban mai ba shawara ga gwamnan na musamman kan harkokin yada labarai, ya bayyana cewa shugabannin jihohin za su hadu a ranar Talata, 6 ga watan Yuli, da Laraba 7 ga watan Yuli, in ji The Guardian.

KU KARANTA KUMA: Kotun Abuja ta aika tsohon shugaban JAMB kurkuku, ta kuma bayyana dalilin yanke hukuncin

Hotuna sun bayyana yayin da gwamnonin arewa maso gabas suka isa Taraba don ganawa mai muhimmanci
Gwamnonin arewa maso gabas za su yi ganawa mai muhimmanci a Taraba Hoto: @HarunaManu247
Asali: Facebook

Wani babban jami’in tsaro ya jaddada shirin jihar na taron, ya kara da cewa an samar da isasshen tsaro.

A cewar jaridar Leadership, Abu ya bayyana cewa gwamnonin za su tattauna batutuwan da ke hana ci gaban jihohi shida na yankin, tsaro, ci gaban tattalin arziki, da kalubalen zamantakewar.

Legit.ng ta tattaro cewa an hangi gwamnonin da aka zaba a karkashin jam'iyyun Peoples Democratic Party (PDP) da All Progressives Congress (APC) a filin jirgi.

KU KARANTA KUMA: Shugaban kasa a 2023: Tana shirin karewa Atiku, Kwankwaso, Tambuwal da sauransu

Manyan bakin sun hada da Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi, Gwamna Muhammed Inuwa Yahaya na jihar Gombe da kuma gwamna Babagana Zulum na jihar Borno tare da mataimakin gwamnan jihar Taraba, Haruna Manu.

Bayan Taro a Lagos, Gwamnonin Kudu Sun Kafa Sharaɗi Ga Dukkan Jami'an Tsaro

A wani labari na daban, gwamnonin kudancin ƙasar nan sun bayyana cewa daga yanzun ya zama wajibi idan jami'an tsaro zasu cafke wani ɗan yankin su sanar da gwamnan jihar, kamar yadda premium times ta ruwaito.

A yan kwanakin nan ne dai, jami'an tsaro na farin kaya (DSS) suka mamaye gidan mai fafutukar kafa ƙasar yarbawa, Sunday Igboho, inda suka kashe mutum biyu.

Gwamna Seyi Mekinde, wanda yayi jawabi a shafinsa na dandalin sada zumunta, yace sun tattaunawa abubuwan da suka shafi ƙasa da dama a taron da suka gudanar a jihar Lagos.

Asali: Legit.ng

Online view pixel