Saƙo ga gwamnonin Kudu: Dole ɗan ƙabilar Igbo ne zai zama shugaban ƙasa, cewar Ohanaeze

Saƙo ga gwamnonin Kudu: Dole ɗan ƙabilar Igbo ne zai zama shugaban ƙasa, cewar Ohanaeze

  • Kungiyar Ohanaeze Ndigbo ta bukaci gwamnonin kudu da su mika wa yankin kudu maso gabas shugabancin 2023
  • Wannan na zuwa ne yayin da gwamnonin suka aika sako a bayyane zuwa yankin arewa cewa dole ne shugaban Najeriya na gaba ya fito daga yankin kudu
  • A cewar kungiyar ta Ohanaeze, mika shugabancin kasar zuwa yankin kudu maso gabas zai ba da damar buga wasan da kyau da adalci

Kungiyar koli ta kabilar Ibo wato Ohanaeze Ndigbo ta aika sako ga gwamnonin kudu.

Sakon mai sauki ne - ya kamata shugaban kasa mai zuwa ya fito daga kudu maso gabas, jaridar Punch ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Shugaban kasa a 2023: Tana shirin karewa Atiku, Kwankwaso, Tambuwal da sauransu

Saƙo ga gwamnonin Kudu: Dole ɗan ƙabilar Igbo ne zai zama shugaban ƙasa, cewar Ohanaeze
Kungiyar Ohanaeze ta roki gwamnonin kudu da su bar wa dan Ibo shugabancin kasa a 2023 Hoto: Rotimi Akeredolu
Asali: Facebook

Kungiyar Ohanaeze Ndigbo ta fadawa gwamnonin kudu cewa yankin kudu maso gabas ce ya kamata ta samar da shugaban kasa na gaba.

A cewar mai magana da yawun kungiyar Ohanaeze, Alex Ogbonnia, wannan zai bayar da damar buga wasa mai kyau da adalci.

KU KARANTA KUMA: Bayan Ya Sallame Su, Gwamna Matawalle Ya Amince da Maida Mutum 8 Muƙamansu

Ya ce:

“Don haka adalci, daidaito da gaskiya za su bukaci su amince su mika Shugabancin ga Kudu maso Gabas. Don haka wajen yi musu godiya, za mu ci gaba da roƙon su da su yi la’akari da Kudu Maso Gabas ta samu Shugabancin Kasar.”

Yankin mu ya kamata ya fitar da shugaban kasa na gaba, Gwamnonin Kudu

A baya mun ji cewa Gwamnonin jihohin kudancin Nigeria 17 sun amince kan cewa shugaban kasar Nigeria na gaba a shekarar 2023 ya kamata ya fito daga yankinsu ne kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Hakan na dauke ne cikin sakon bayan taro da kungiyar gwamnonin kudun ta fitar bayan taron ta da aka yi a gidan gwamnatin Legas da ke Alausa, ranar Litinin.

Daily Trust ta ruwaito cewa sun kuma cimma matsayar cewa ya kamata a rika kama-kama ne tsakanin kudu da arewa wurin zaben shugaban kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel