Kotun Abuja ta aika tsohon shugaban JAMB kurkuku, ta kuma bayyana dalilin yanke hukuncin
- Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta dawo da sauraren karar da ake yi kan Farfesa Dibu Ojerinde, tsohon shugaban JAMB
- Hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta da sauran hukumomin da ke da alaka da su ne suka gurfanar da farfesan
- Hukumar yaki da cin hanci da rashawar ta yi ikirarin cewa Ojerinde yana da tambaya da zai amsa game da zargin karkatar da kudade a NECO
Biyo bayan umurnin kotu, an tsare Farfesa Dibu Ojerinde, tsohon shugaban hukumar shirya jarrabawar shiga jami'o'i (JAMB) a gidan yari.
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ce ta bayar da wannan umarnin a ranar Talata, 6 ga watan Yuli, har zuwa lokacin da za a saurari bukatar neman belinsa, wanda aka shirya yi a ranar 8 ga watan Yuli, jaridar The Nation ta ruwaito.
KU KARANTA KUMA: Abubakar Malami ya musanta wallafa rubutun batanci a kan Igbo da Hausawa
Tuhumar da ake yiwa tsohon Shugaban na JAMB
Ojerinde na fuskantar tuhume-tuhume 18 na hadin baki wajen karkatar da kudaden gwamnati da aka kiyasta ya kai N900 miliyan wanda Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta ICPC ta ke yi masa.
ICPC ta fadawa kotun cewa Farfesan ya aikata laifukan da ake zargin sa da shi lokacin da ya ke aiki a matsayin shugaban Hukumar Jarrabawar ta Kasa (NECO).
Sai dai Ojerinde, ya musanta aikata laifin yayin da aka karanto masa tuhumar.
Alkali ya ki amincewa da neman belin da Ojerinde yayi ta fatar baki
Jaridar PM News ta ruwaito cewa lauyan nasa ya yi kokarin shawo kan mai shari’a Obiora Egwuatu don bai wa Ojerinde damar ci gaba da belin da aka ba shi, amma alkalin ya ki amincewa da bukatar bayan lauyan ICPC, Ebenezer Shogunle, ya nuna adawa da bukatar.
ICPC Ta Kama Tsohon Shugaban JAMB Kan Almundahar N900m
Hukumar Yaki da rashawa ta ICPC ta kama tsohon Rajistara kuma shugaban hukumar shirya jarrabawar shiga jami'o'i, JAMB, Farfesa Dibu Ojerinder kan zarginsa da bannatar da Naira miliyan 900.
Ana zargin Ojerinde da aikata laifuka na almundaha yayin da ya ke shugabancin hukumar JAMB da Hukumar Shirya Jarrabawar Kammala Sakandare ta Kasa, NECO, rahoton The Nation.
An kama shi ne a ranar 15 ga watan Maris na 2021 a babban birnin tarayya, Abuja kamar yadda kakakin hukumar ICPC, Mrs Azuka C. Ogugua ta sanar.
Asali: Legit.ng