Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 2, Sun Yi Awon Gaba da Shanu da Dama a Jihar Katsina

Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 2, Sun Yi Awon Gaba da Shanu da Dama a Jihar Katsina

  • Yan bindiga sun sake kai hari jihar Katsina, inda suka hallaka mutum 2, sannan suka yi awon gaba da shanu
  • Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun mamaye ƙauyukan Ajiya da Yasore da sanyin safiyar Lahadi
  • Magajin garin Yasore, Abdurazak Mamman, ya tabbatar da harin a garinsa, yace an kashe wani manomi

Wasu yan bindiga sun kai hari ƙauyukan Ajiya da Yasore dake ƙaramar hukumar Batsari, jihar Katsina, inda suka hallaka mutum biyu tare da awon gaba da shanu 35.

KARANTA ANAN: Bayan Ya Sallame Su, Gwamna Matawalle Ya Amince da Maida Mutum 8 Muƙamansu

Wata majiya mai ƙarfi ta shaida wa jaridar leadership cewa maharan sun mamaye ƙauyen ranar Lahaɗi da safe ɗauke da manyan makamai.

Yan bindigan sun harbe mutum biyu har lahira yayin da suka jikkata wasu mutane da dama da harbin bindiga.

Yan bindiga sun kai hari jihar Katsina
Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 2, Sun Yi Awon Gaba da Shanu da Dama a Jihar Katsina Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Majiyar tace: "Mutane ɗauke da manyan makamai sun kai hari ƙauyukan da sanyin safiyar lahadi, inda suka buɗe wuta, sun kashe mutum biyu yayin da suka bar wasu da dama da raunin harbin bindiga."

Magajin garin Yasore ya tabbatar da harin

Magajin Yasore, Abdurazak Mamman, ya tabbatar da kai harin, yace: "Maharan sun farmaki wanda aka kashe ne yayin da yake aiki a gonarsa, inda suka kashe shi sannan suka yi awon gaba da shanunsa."

KARANTA ANAN: Bayan Taro a Lagos, Gwamnonin Kudu Sun Kafa Sharaɗi Ga Dukkan Jami'an Tsaro

Mamman yayi kira ga gwamnatin jihar da ta yi iyakacin ƙoƙarinta ta samar da zaman lafiya a yankin domin manoma su cigaba da sana'arsu cikin kwanciyar hankali.

A wani labarin kuma El-Rufa'i Ya Yi Magana Kan Sace Ɗalibai da Yan Bindiga Suka Sake Yi a Jihar Kaduna

Gwamna El-Rufa'i na jihar Kaduna, ya nuna rashin jin dadinsa bisa lamarin da ya faru na sace ɗalibai kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Gwamnan ya bayyana harin yan bindigan a matsayin wani aikin sheɗanci da kokarin hana karatu a Kaduna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262