Bayan Ya Sallame Su, Gwamna Matawalle Ya Amince da Maida Mutum 8 Muƙamansu
- Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle ya amince da naɗin wasu masu bashi shawara ta musamman mutum 8
- Waɗanda aka naɗa ɗin suna daga cikin tsofaffin mashawartansa da ya sallama a baya
- Gwamnan yace sake naɗin na su zai fara aiki ne daga ranar da aka amince su koma bakin aiki
Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara, a ranar Litinin, ya amince da sake naɗa masu bashi shawara ta musamman 8 daga cikin waɗanda ya kora a baya, kamar yadda vanguard ta ruwaito.
KARANATA ANAN: Bayan Taro a Lagos, Gwamnonin Kudu Sun Kafa Sharaɗi Ga Dukkan Jami'an Tsaro
Wannan na ƙunshe ne a cikin wani jawabi da sakataren al'amuran yan majalisar zartarwa, Yakubu Haidara, ya fitar a madadin muƙaddashin sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Kabiru Balarabe.
Rahoton PM News ya nuna cewa, waɗanda aka maida kan muƙaman nasu sun haɗa da, Aminu Abdullahi Alkali, Ahmed Muktar Mohammed da kuma Junaidu Aminu Ƙaura.
Sauran sun haɗa da, Ibrahim Ma'aji Gusau, Dr. Aslam Aliyu, Yusuf Abubakar Zugu, Ɗanyaro Abdullahi Wuya, da kuma Abubakar Musa Mainera.
Haidara, yace: "Wannan naɗin nasu zai fara aiki ne nan take, ba tare da ɓata lokaci ba."
KARANTA ANAN: Yanzu-Yanzu: Ministan Shugaba Buhari Ta Yanke Jiki Ta Faɗi a Wurin Taro
A baya gwamnan ya sallami mashawartansa gaba ɗaya
A kwanakin baya, Gwamna Matawalle, ya sallami gaba daya masu ba shi shawara ta musamman in banda mutum ɗaya.
"Gwamna Bello Matawalle ya sallami dukkan masu bashi shawara ta musamman daga kan muƙamansu, amma banda mai bada shawara kan tsaro." Inji Alhaji Kabiru Balarabe, Sakataren gwamnati na riƙo.
A wani labarin kuma Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Shugaban Ƙungiyar Ƙwadugo NLC
Wasu yan bindiga da ba'a san ko suwaye ba sun yi awon gaba da shugaban ƙungiyar ƙwadugo NLC reshen jihar Taraba , Peter Jediel.
Wannan shine karo na biyu da aka sace shugaban NLC na jihar Taraba, inda a baya ma wasu yan bindiga suka yi garkuwa da shi.
Asali: Legit.ng