El-Rufa'i Ya Yi Magana Kan Sace Ɗalibai da Yan Bindiga Suka Sake Yi a Jihar Kaduna

El-Rufa'i Ya Yi Magana Kan Sace Ɗalibai da Yan Bindiga Suka Sake Yi a Jihar Kaduna

  • Gwamna El-Rufa'i na jihar Kaduna, ya nuna rashin jin dadinsa bisa lamarin da ya faru na sace ɗalibai
  • Gwamnan ya bayyana harin yan bindigan a matsayin wani aikin sheɗanci da kokarin hana karatu a Kaduna
  • Jami'an tsaro sun samu nasarar kuɓutar da wasu daga cikin ɗaliban, yayin da suke cigaba da bincike

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i yayi Allah wadai da sace ɗaliban makarantar sakandiren Bethel Baptist Dimishi, ƙaramar hukumar Chukun, jihar Kaduna, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Yanzu-Yanzu: Ministan Shugaba Buhari Ta Yanke Jiki Ta Faɗi a Wurin Taro

Kwamishinan tsaro da al'amuran cikin gida na jihar, Samuel Aruwan, shine ya bayyana haka a wani jawabi da ya fitar.

A cikin jawabin, Gwamna El-Rufa'i, ya bayyana lamarin da wani aikin sheɗanci da kuma ƙoƙarin gurgunta ɓangaren Ilimi a jihar, kamar yadda punch ta ruwaito.

Malam Nasiru El-Rufa'i
El-Rufa'i Ya Yi Magana Kan Sace Ɗalibai da Yan Bindiga Suka Sake Yi a Jihar Kaduna Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Yace: "Wannan aikin sheɗanci ne da ƙoƙarin hana yara samun ilimi, kuma ba zamu bar haka ta cigaba da faruwa ba."

Rahotanni sun bayyana cewa da safiyar yau Litinin ne, wasu yan bindiga suka mamaye makarantar Bethel Baptist, inda suka yi awon gaba da ɗalibai da dama.

Jami'an tsaro sun ƙwato wasu daga cikin ɗaliban

Wata tawagar sojoji da yan sanda sun ɗauki matakin gaggawa inda suka kai ɗauki makarantar domin hana maharan aiwatar da mummunan nufinsu.

A wani rahoto da muka samu daga hukumomin tsaro ya nuna cewa, sun kuɓutar da ɗalibai 28 yayin da ɓarayin suka yi awon gaba da wasu da ba'a san adadin su ba.

KARANTA ANAN: Da Ɗuminsa: Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Shugaban Ƙungiyar Ƙwadugo NLC

Hukumomin tsaro sun baiwa gwamnatin Kaduna tabbacin zasu yi iya ƙoƙarin su su kuɓutar ɗaliban baki ɗaya.

Tun bayan faruwar lamarin, gwamna El-Rufa'i, ya cigaba da bibiyar lamarin kuma ana aike masa da rahoto duk bayan awa ɗaya.

A wani labarin kuma Gwamna Masari Ya Rushe wasu Gine-Gine a Jiharsa, Yace Sun Saɓa Wa Doka

Hukumar tsara birane da karkara ta jihar Katsina , (URPB) ta rushe wasu gine-gine da aka yi su ba bisa ƙa'ida ba a yankin Morawa, ƙaramar hukumar Ɓatagarawa, jihar Katsina.

Kakakin ma'aikatar ƙasa ta jihar, Alhaji Yakubu Lawal, shine ya bayyana haka a wani jawabi da ya fitar ranar Lahadi a Katsina.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262