Bayan Taro a Lagos, Gwamnonin Kudu Sun Kafa Sharaɗi Ga Dukkan Jami'an Tsaro

Bayan Taro a Lagos, Gwamnonin Kudu Sun Kafa Sharaɗi Ga Dukkan Jami'an Tsaro

  • Gwamnonin Kudu sun kafa wani sharaɗi ga hukumomin tsaro ƙafin su kama wani a yankin su
  • Gwamnonin sun ce daga yanzun duk lokacin da jami'am tsaro zasu kama wani sai sun nemi izini
  • Sun bayyana cewa bayan kammala mulkin shugaba Buhari, ɗan yankin su ne zai gaje shi

Gwamnonin kudancin ƙasar nan sun bayyana cewa daga yanzun ya zama wajibi idan jami'an tsaro zasu cafke wani ɗan yankin su sanar da gwamnan jihar, kamar yadda premium times ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Yanzu-Yanzu: Ministan Shugaba Buhari Ta Yanke Jiki Ta Faɗi a Wurin Taro

A yan kwanakin nan ne dai, jami'an tsaro na farin kaya (DSS) suka mamaye gidan mai fafutukar kafa ƙasar yarbawa, Sunday Igboho, inda suka kashe mutum biyu.

Gwamna Seyi Mekinde, wanda yayi jawabi a shafinsa na dandalin sada zumunta, yace sun tattaunawa abubuwan da suka shafi ƙasa da dama a taron da suka gudanar a jihar Lagos.

Taron gwamnonin Kudu a Lagos
Daga Yanzu Duk Jami'an Tsaron da Zasu Cafke Wani a Yankin Mu Sai Sun Sanar Mana, Gwamnonin Kudu Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Yace: "A taron mu na gwamnonin kudu, mun tattauna batutuwa da dama da suka shafi ƙasa da suka haɗa da ƙara jaddada buƙatar samar da yan sandan jihohi."

"Sannan Mun cimma matsayar cewa duk wata hukumar tsaro da zata yi wani aiki a yankin mu, ya wajaba su sanar da gwamnan jihar da zasu yi aikin."

"Hakanan mun amince kowane gwamna ya samar da dokar hana kiwo a hukumance kafin 1 ga watan Satumba 2021."

KARANTA ANAN: El-Rufa'i Ya Yi Magana Kan Sace Ɗalibai da Yan Bindiga Suka Sake Yi a Jihar Kaduna

Shugaban ƙasa na gaba daga yankin mu zai fito

A ƙarshen taron da ya gudana a jihar Lagos ranar Litinin, gwamnonin sun fitar da wata sanar wa cewa yankin kudu ne ya kamata ya fiyar da shugaban ƙasa na gaba, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Hakazalika gwamnonin sun bayyana cewa ƙungiyarsu a zata cigaba da aiki tuƙura dan tabbatar da zaman Najeriya ƙasa ɗaya.

A wani labarin kuma Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Shugaban Ƙungiyar Ƙwadugo NLC

Wasu yan bindiga sun samu nasarar awon gaba da shugaban ƙungiyar NLC na jihar Taraba, Peter Jediel.

Rahoto ya nuna cewa maharan sun mamaye gidansa ne da safiyar Lahadi a garin Sunkani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel