Ku gaggauta ceto dukkan dalibai da aka sace, Buhari ga hukumomin tsaro

Ku gaggauta ceto dukkan dalibai da aka sace, Buhari ga hukumomin tsaro

  • Shugaban kasa ya umarci sojoji, 'yan sanda da sauran hukumomin tsaro da su ceto dalibai da aka sace da gaggawa
  • Buhari yace satar dalibai da 'yan bindiga ke yi tsabar rangwanta ce da kuma cin zarafi ga iyaye da kasar nan baki daya
  • Shugaban ya koka da yadda 'yan bindigan ke barazana ga ilimi a yankin arewaci wanda dama can sune koma-baya

Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci sojoji, 'yan sanda da sauran hukumOmin tsaro da su tabbatar da gaggauta ceto dukkan wadanda aka sace.

Buhari ya bada wannan umarnin ne a ranar Litinin ta wata takarda da Garba Shehu ya fitar a Facebook inda ya nuna damuwarsa kan harin jihohin Kaduna da na Neja wanda yace duk dalibai aka kwashe.

A yayin tabbatar da ci gaba da tura karin jami'ai dukkan yankunan da ke da matsala, shugaban kasan yayi kira ga hukumomin tsaron da su yi aikin gaggawa wurin ceto dukkan 'yan makarantan a jihohin tare da dawo dasu gida lafiya.

KU KARANTA: Ba zan yi murabus daga siyasa ba har sai na mutu, Malam Shekarau

Ku gaggauta ceto dukkan dalibai da aka sace, Buhari ga hukumomin tsaro
Ku gaggauta ceto dukkan dalibai da aka sace, Buhari ga hukumomin tsaro. Hoto daga thecableng
Asali: UGC

Satar dalibai ragwanci ne da cin zarafin kasa

Shugaban kasan ya kwatanta sace jama'an da aikin ragwancI tare da cin zarafi ga iyalai da kasar baki daya.

Buhari ya ce lamarin satar dalibai a jihohin arewa tuni ya zama barazana ga habaka saka yara makaranta a jihohin yankunan duk da sune koma baya.

Ya yi kira ga gwamnatocin jihohin da su tabbatar sun bi shirin majalisar dinkin duniya ta baiwa makarantu kariya wanda gwamnatin nan ta runguma.

KU KARANTA: Dama na sha alwashin kai ka kasa, Asari Dokubo yayi martani kan kamen Nnamdi Kanu

'Yan bindiga sun sace dalibai a Kaduna

A ranar Litinin ne wasu da ake zargin 'yan bindiga ne suka shiga Bethel Baptist High School dake Damishi a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna kuma suka sace dalibai.

An gano cewa 'yan bindigan sun kutsa makarantar wurin karfe 2 na dare. Amma kuma dalibai 26 cikin wadanda aka sace 'yan sanda sun ceto su.

Wannan ne lamari na biyu daga cikin garkuwa da mutane da aka yi a jihar cikin sa'o'i 24.

A kalla mutum takwas aka sace a ranar Lahadi bayan 'yan bindiga sun kai farmaki asibitin kutare dake Zaria.

A wani labari na daban, hukumar kula da al'amuran 'yan sanda ta shirya tsaf domin yi wa Ibrahim Magu, tsohon mukaddashin shugaban hukumar yaki da rashawa da hana yi wa kasa zagon kasa (EFCC), karin girma zuwa mataimakin sifeta janar na 'yan sanda a wannan makon, TheCable ta fahimci hakan.

Magu, wanda aka karawa girma zuwa kwamishinan 'yan sanda a 2018, an bukaci cireshi daga matsayin shugaban EFCC bayan kammala binciken kwamitin Jastis Ayo Salami bayan an zargesa da yin amfani da kujerarsa ba yadda ya dace ba.

Kwamitin ya bukaci a tsige Magu daga kujerarsa saboda kasa bayyana inda kudade har N431,000,000 na kudin yada labarai da aka sakarwa ofishin shugaban hukumar EFCC tsakanin watan Nuwamba na 2015 zuwa Mayun 2020 suke.

Asali: Legit.ng

Online view pixel