Dalla-dalla: Za a yi wa Magu karin girma zuwa AIG duk da zargin rashawa

Dalla-dalla: Za a yi wa Magu karin girma zuwa AIG duk da zargin rashawa

  • An gano cewa hukumar kula da al'amuran 'yan sanda na shirin karawa Ibrahim Magu girma zuwa AIG
  • Ibrahim Magu shine tsohon shugaban hukumar EFCC da aka tsige sakamakon zarginsa da rashawa
  • Kamar yadda kwamitin Jastis Salami ya fitar, an gano cewa Magu yayi amfani da kujerarsa wurin rub da ciki kan N431m

Hukumar kula da al'amuran 'yan sanda ta shirya tsaf domin yi wa Ibrahim Magu, tsohon mukaddashin shugaban hukumar yaki da rashawa da hana yi wa kasa zagon kasa (EFCC), karin girma zuwa mataimakin sifeta janar na 'yan sanda a wannan makon, TheCable ta fahimci hakan.

Magu, wanda aka karawa girma zuwa kwamishinan 'yan sanda a 2018, an bukaci cireshi daga matsayin shugaban EFCC bayan kammala binciken kwamitin Jastis Ayo Salami bayan an zargesa da yin amfani da kujerarsa ba yadda ya dace ba.

KU KARANTA: Kaduna: 'Yan bindiga sun sheke mutum 7, sun sace wasu 10 a sabon hari

Dalla-dalla: Za a yi wa Magu karin girma zuwa AIG duk da zargin rashawa
Dalla-dalla: Za a yi wa Magu karin girma zuwa AIG duk da zargin rashawa. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Kwamitin ya bukaci a tsige Magu daga kujerarsa saboda kasa bayyana inda kudade har N431,000,000 na kudin yada labarai da aka sakarwa ofishin shugaban hukumar EFCC tsakanin watan Nuwamba na 2015 zuwa Mayun 2020 suke.

An zargesa da bata da duk wata shaida tare da hanawa tare da dakile duk wasu hanyoyin bincike a wani bincike da ake yi da ya hada da tsohon shugaban majalisar tarayya da tsohon manajan darakta PPMC.

KU KARANTA: Iyaye sun fusata kan dalilin El-Rufai na cire dan shi daga makarantar gwamnati

Amma kuma, bayan da kwamitin ya mika rahoton a watan Nuwamban 2020, kadan daga cikin shawarwarinsu aka aiwatar.

Magu, wanda har yanzu bai saki jiki ba bayan binciken kwamitin, an gano cewa yana da alaka mai kyau da shugaban hukumar kula da lamurran 'yan sanda, Musiliu Smith, tsohon sifeta janar na 'yan sanda daga jihar Legas.

Wasu manyan jami'an 'yan sanda an gano suna ta guna-guni kan rashin ladabtar da Magu wanda ya dinga musanta zarginsa da ake yi.

A watan Augustan 2020, TheCable ta bayyana cewa kwamitin ya bukaci a sallami Magu kuma an gurfanar dashi kan zargin rashawa da amfani da kujerarsa ba yadda ya dace ba.

A wani labari na daban, miyagun 'yan bindiga dauke da makamai sun kutsa yankin Katsit na karamar hukumar Zangon Kataf ta jihar Kaduna.

A kalla mutum uku ne suka samu miyagun raunika yayin harin da ya faru a daren Lahadi, Daily Trust ta ruwaito.

Daily Trust ta tattaro cewa, bayan 'yan bindigan sun shiga yankin, sun fara harbe-harbe babu kakkautawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng